Buni Vs Sherrif: Takaitaccen Bayani Game Da Manyan ‘Yan Takarar Gwamnan Jihar Yobe a Zaben Gobe
- A ranar 18 ga watan Maris na 2023, za a shirya zaben Gwamna a Yobe da wasu Jihohin Najeriya
- Mai Mala Buni yana neman tazarce a Jam’iyyar APC, zai fuskanci ‘Dan takaran da ya tsaya a PDP
- Tun shekarar 1999, jam’iyyar hamayya ta PDP ba ta taba samun damar yin mulki a Borno da Yobe ba
A rahoton nan, mun tattaro bayanai game da manyan masu neman takarar kujerar Gwamna a Yobe.
1. Mai Mala Buni
Haihuwa, karatu da sana’a
Asalin Mai Mala Buni CON mai shekara 55 mutumin Buni Yadi ne a karamar hukumar Gujba. ‘Dan siyasar ya yi firamare da sakandare ne a garin Buni da Goniri.
Kafin shiga siyasa, Mala Buni ya nemi kudi ta harkar kasuwanci da sufuri, ya bude kamfanoni.
Bayan shiga siyasa, ya yi digirin farko a jami’ar Espan Formation University a Benin, daga baya ya samu Digirgir a ilmin huldar kasashen waje daga jami’ar Leeds.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Siyasa
A lokacin mulkin soja a shekarar 1992, Buni ya yi takarar Kansilan Buni a jam’iyyar NRC kuma ya samu nasara. A 2000 ya zama Hadimin ‘dan majalisar tarayya.
A 2004 gwamnatin tarayya ta ba Buni mukami a majalisar kula da jami’ar Uyo. Zuwa 2006, ya zama shugaban jam’iyyar ADC ta reshen Yobe kafin ta hade da AC.
Tsakanin 2007 da 2010, ‘dan siyasar ya karbi shugabancin Jam’iyyar AC. Zuwa 2011 ya shiha ANPP, ya zama Mai ba Ibrahim Gaidam shawara a sha’anin siyasa.
Bayan zamansa Sakataren ANPP a Jihar Yobe, ya zama shugaban APC na farko a Yobe.
Watanni bayan kafa jam’iyyar ta APC, Buni ya zama sakatarenta na kasa zuwa 2018. Bayan nan ya nemi tikitin APC, ya kuma lashe takarar Gwamna a 2019.
2. Shariff Abdullahi
Alhaji Shariff Abdullahi ne yake neman kujerar Gwamna a jihar Yobe a jam’iyyar PDP. ‘Dan siyasar ya samu tikiti a zaben gwani da aka yi a Agustan 2022.
Shariff Abdullahi mai kuri’u 295 a zaben tsaida ‘dan takaran ya yi galaba a kan Dr. Ali Adamu Tikau da ya ci 129 da kuma Abba Gana da ya lashe kuri’u 109.
‘Dan siyasar ya taba zama ‘dan majalisar wakilan tarayya a Najeriya. A zaben 2019, ya nemi kujerar Sanatan Yobe ta Arewa amma Ahmad Lawan ya doke shi.
Baya ga haka, Shariff ya taba zama shugaban karamar hukumarsa. Abokin gaminsa a neman Gwamna a jam’iyyar PDP shi ne Abubakar Bashir Sadiq.
Zaben Yobe a 2023
A mako mai zuwa, ‘dan siyasar zai jarraba sa’arsa a kan surukin tsohon Gwamna, Ibrahim Gaidam da tsohon shugaban Najeriya, Janar Sani Abacha.
Sauran ‘yan takaran Gwamna a Yobe a zaben 18 ga watan Maris sun hada da Garba Umar da ya fito da NNPP, da Malam Ya’u Sabo na jam’iyyar AA.
Asali: Legit.ng