Zaben 18 Ga Watan Maris: Kungiyar CAN Reshen Neja Ta Bukaci Kiristoci Su Zabi Cancanta
- An bukaci kiristoci a jihar Neja da su yi zabe cikin hikima a zaben gwamna mai zuwa
- Kungiyar Kiristocin Najeriya reshen jihar Neja ce ta aika sakon kwanaki biyar kafin zaben gwamna na ranar 18 ga watan Maris
- Daniel Atori, hadimin shugaban kungiyar CAN ya shawarci mabiya addinin da su zabi yan takara wadanda ke da ra’ayi mutane a zuciya
Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) reshen jihar Neja ta yi kira ya Kiristoci a jihar da su zabi yan takarar da suka cancanta kawai a zaben gwamna da na yan majalisar jiha na ranar Asabar, 18 ga watan Maris.
A wata sanarwa da Kakakin shugaban CAN, Daniel Atori ya saki, ya bukaci masu zabe da kada su yi zabe bisa la’akari da jam’iyyun siyasa maimakon haka su zabi yan takarar da suka cancanta kuma masu ra’ayin mutane a zuci, rahoton Vanguard.
CAN ta baiwa Kiristocin Neja aiki gabannin zaben gwamna
Atori ya ce:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
“Muna kira ga kowa da ya zabi yan takarar da kuke ra’ayi wadanda za su tabbatar da bai wa mutane ilimi mai inganci da kiwon lafiya kyauta.”
Kada ku zabi yan takarar da ba a san tushen arzikinsu ba, APC ga al'ummar Ogun
A wani ci gaban, jam'iyyar All Progressives Congress (APC), mai mulki a jihar Ogun ta yi kira ga mazauna da su guji zabar yan takarar da ba a san tushen arzikinsu ba a zaben gwamna na ranar Asabar, 18 ga watan Maris.
Da take bayyana cewa jihar Ogun ba na siyarwa bane, APC ta yi zargin cewa wasu yan takara da suka tara dukiya ta hanyar haram suna kokarin siye kuri'un jama'a a zaben gwamna mai zuwa.
Ta bukaci jama'ar jihar da su zabi Dapo Abiodun da dukannin yan takarar APC domin samun amfani sosai a gwamnatin zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Shugaban majalisar dattawa na 10: Ohanaeze ta marawa Umahi baya
A wani labari na daban, kungiyar dattawan kudu masu gabas, Ohanaeze Ndigbo ta ayyana goyon bayanta ga takarar Gwamna David Umahi na son kujerar shugaban majalisar dattawa a majalisar dokoki ta 10.
Asali: Legit.ng