Jam'iyyar APC Zata Sanya Labule Da Zababbun Ƴan Majalisun Ta

Jam'iyyar APC Zata Sanya Labule Da Zababbun Ƴan Majalisun Ta

  • Jam'iyyar APC ta ƙasa zata sanya labule da zaɓaɓɓun ƴan majalisar wakilai da sanatocin jam'iyyar
  • Zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Asiwaju Bola Tinubu da mataimakin sa, Kashim Shettima za su halarci taron
  • Taron dai ana hasashen baya rasa nasaba da zaɓen sababbin shugabannin majalisar wakilai da ta dattawa

Abuja- Zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, da shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na ƙasa, Abdullahi Adamu, za su gana da zaɓaɓɓun ƴan majalisun tarayya na jam'iyyar a ranar Litinin.

A cewar wata sanarwa da ofishin sakataren jam'iyyar na ƙasa, Iyiola Omisore, ya fitar, zaɓaɓɓen mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, zai kasance a wajen taron. Rahoton Premium Times.

Adamu
Jam'iyyar APC Zata Sanya Labule Da Zababbun Ƴan Majalisun Ta Hoto: Punch
Asali: UGC

Taron zai kasance ne a ɗakin taro na Banquet Hall a fadar shugaban ƙasa sannan an shawarci ƴan majalisun da su iso wajen taron da rana.

Kara karanta wannan

Akwai Matsala: Tana Ƙasa Tana Dabo Kan Yiwuwar Ƙidayar Bana, Hukumar Tayi Ƙarin Haske

Jam'iyyar ta kuma umurci zaɓaɓɓun ƴan majalisun da su zo wajen taron tare da satifiket ɗin lashe zaɓen su. Rahotn Channels Tv

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Ana sanar da dukkanin zaɓaɓɓun sanaatoci da zaɓaɓɓun ƴan majalisar wakilai na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), cewa ana gayyatar su taro da shugabannin jam'iyyar na ƙasa.

Sanarwar na cewa:

“Taron wanda zai samu halartar zaɓaɓɓen shugaban ƙasa da mataimakin sa zai auku ne a ɗakin taro na Banquet Hall, na fadar Aso Rock, Abuja."
"Dole ne zaɓaɓɓun sanatoci da ƴan majalisar wakilai su zo wajen taron su kaɗai tare da satifiket ɗin lashe zaɓe da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta basu."
Duk da dai ba a bayyana abinda za a tattauna a wajen taron ba a cikin takardar gayyatar, an samo cewa za ayi taron ne akan zaɓen shugabannin majalisar dattawa ta 10 da majalisar wakilai, waɗanda za a ƙaddamar a watan Yuni.

Kara karanta wannan

Hotuna Sun Bayyana Yayin Da INEC Ta Ba Zababbun Ƴan Majalisar Wakilai Satifiket Ɗin Cin Zaɓe

A bisa sakamakon zaɓen da hukumar INEC ta bayyana, jam'iyyar APC, tana da rinjaye a majalisun biyu.

A majalisar wakilai, APC tana da kujeru 162 daga cikin 325 da aka bayyana sakamakon zaɓen su. Jam'iyyar ta kuma samu kujeru masu rinjaye a majalisar dattawa inda take da guda 57.

Kudu Maso Gabas Na Iya Samun Shugaban Majalisar Dattawa Yayin da Tinubu Ke shirin Kafa Gwamnatin Hadin Kai

A wani labarin na daban kuma, yankin Kudu maso Gabas na iya samun shugabancin majalisar dattawa a gwamnatin Tinubu.

Zaɓaɓɓen shugaban ƙasar na son kafa gwamnati wacce zata tafi da kowane yanki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng