Naira: Rashin Bin Umurnin Kotu Ka Iya Haddasa Rashin Zaman Lafiya, Kungiyar Arewa Ta Gargadi Buhari
- Zauren tuntuba ta Arewa sun gargadi Shugaban kasa Muhammadu Buhari kan abunda ka iya kaiwa ya komo kan batun Naira
- ACF ta ce kin bin umurnin kotun koli na amincewa da ci gaba da amfani da tsoffin kudi na iya haifar da rikici a kasar
- Kungiyar ta ce wajibi ne ta fada wa Buhari gaskiya kasancewar sun dade suna mara masa baya
Kungiyar tuntuba ta arewa (AGF) ta yi gargadin cewa ci gaba da kin bin umurnin kotun koli dangane da amfani da tsoffin kudi na iya haddasa rikici a kasar jaridar Daily Trust ta rahoto.
A wata sanarwa da ya saki, babban sakataren kungiyar ta ACF, Murtala Aliyu, ya yarda da matakin gwamnonin jiha wadanda suka maka gwamnatin tarayya a kotu kan manufar.
Tsarin aiwatar da manufar sauya kudi na CBN ya saba wa doka, ACF
Ya ce yanayin yadda babban bankin Najeriya (CBN) ke tafiyar da lamura a yanzu ya haifar da damuwa game da yancin yan Najeriya kasancewar ya shafi yancinsu na samun kudaden shiga ta hanyar da suke so.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Jaridar The Sun ta nakalto kungiyar na cewa:
"Duk abun da CBN ko wani ya ce game da amfanin wannan manufar wanda a zahirin gaskiya suna da yawa, bai da wani tasiri sosai daga lokacin da babban kotun kasar ta yanke hukunci a kai, akalla dai tsarin da aka bi wajen aiwatar da shi ya saba doka.
"Kwanaki goma sun yi wa gwamnati tsawo da za ta nemi hanyar bin umurnin kotu wacce ita ce cibiyar cimma zaman lafiya, bin oda da shugabanci nagari a kasar. Shugaban kasa Buhari ya dauki rantsuwar kare kundin tsarin mulkin Najeriya.
"A matsayinmu na magoya bayansa na tsawon lokaci, bai kyautu a garemu ba idan muka ki gargadinsa cewa amfanin da ake ganin yana tattare da manufar sauya naira ba zai taba wanke barnar da hakan ya yi wa sunansa a matsayinsa na dan damokradiyya kuma mai bin doka ba.
"Wannan na iya tada zaune tsaye a fadin Najeriya. Bamu yarda ba kuma ba za mu iya bashi shawarar sadaukar da wannan babban lamari ba da sunan manufa wanda yawancin yan Najeriya ba su fahimci manufofin ba a halin yanzu."
Ya kuma koka kan dandazon jama'a da dogon layukan da ake yi a bankuna da akwatunan ATM a fadin kasar yayin da mutane ke fafutukar samun sabbin kudi wanda har yanzu basu wadata ba, lamarin da ya haifar da zanga-zanga da sauransu.
Legit.ng ta zanta da wata yar kasuwa a garin Minna da ke jihar Neja inda ta ce lallai wannan manufar na yi masu illa ba kadan ba.
"Na Shiga Uku": Wani Dan Najeriya Ya Koka Bayan Gayyatar Wata Budurwa Ta Kwana A Gidansa, Ya Wallafa Bidiyo
Malama Hajara Alhassan ta ce:
"Ina siyar da kayan abinci kama daga shinkafa, wake, garin masara, manja, man gyara da sauransu, amma kusan sati biyu kenan ana zuwa nema bani da shi.
"A gida nake kasuwancina maimakon zama haka, amma ga shi komai ya kare mun ban da kudin siyan kaya a hannu. Masu zuwa siyayya wurina transfa suke yi mu amma yan kauye basa karbar transfa a wajenmu sai tsaba.
"Ya kamata gwamnati ta duba wannan al'amari musamman saboda mu masu kananan sana'o'i muna gab da rushewa."
A wani labari na daban, mun ji cewa chajin da masu POS ke yi yayin cire kudi ya ruguzo da kaso 90 bayan hukuncin kotun koli da ya bukaci a ci gaba da amfani da tsoffin kudi.
Asali: Legit.ng