Magoya Bayan Tinubu Sun Bayyanawa APC Wanda Suke Son Ya Zama Kakakin Majalisar Dokokin Tarayya Na Gaba

Magoya Bayan Tinubu Sun Bayyanawa APC Wanda Suke Son Ya Zama Kakakin Majalisar Dokokin Tarayya Na Gaba

  • An yi kira ga shugabannin jam'iyyar All Progressives Congress, APC, su tabbata Muktar Betara ya zama kakakin majalisar dokokin tarayya na gaba
  • Wasu kungiyoyin magoya bayan Bola Tinubu ne suka yi wannan kiran na son Betara ya zama kakakin majalisa na 10
  • Kungiyoyin ta bakin shugaban su sun bayyana Betara a matsayin jajirtacce wanda zai bada irin jagorancin da ake bukata a majalisar zubi ta 10

Wata hadakar kungiyoyi masu goyon bayan Tinubu a Najeriya, a ranar Lahadi, 12 ga watan Maris, sun bukaci jam'iyyar APC mai mulki a kasa ta goyi bayan dan majalisa mai wakiltar Biu/Bayo/Shani, Muktar Betara, don zama kakakin majalisar tarayya zubi na 10.

Kungiyar, a yayin taron manema labarai da ta kira a Abuka, ta ce Betara shine mafi cancanta cikin sa'o'insa yan majalisa.

Kara karanta wannan

2023: CAN Ta Fada Wa Kiristoci Yan Takarar Da Za Su Kada Wa Kuri'a A Zaben Gwamnoni Da Majalisar Jiha

Batera
Kungiyoyin Goyon Bayan Tinubu Sun Ce Sun Son A Zabi Hon. Betara a Matsayin Kakakin Majalisa Na Gaba. Hoto: Guardian, Betara
Source: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Da ya ke magana a yayin taron, shugaban hadakar, Moses Ikani, sun bayyana Betara a matsayin dan majalisa wanda ya ke da kwarewa da jajircewa da gaskiya da iya aiki, rahoton The Cable.

Akanta kuma jajirtacce

Ya ce fitaccen akantan kuma za a iya bayyana shi a matsayin dan majalisa mai basira da hazaka wanda ya san kallubalen da ke shugabancin majalisa.

Ya kuma ce Betara ya nuna jajircewa a dukkan ayyukan da ya yi a majalisa tun 2017, Ikana ya ce dan majalisar yana da kwarewa, iyawa da kokari - kuma yana da tsare-tsare don magance kallubalen da ke gaban Majalisar Tarayyar.

Kalamansa:

"Majalisa ita ce muhimmiyar cibiyar dimokuradiyya ne don wakilcin siyasa. Don haka, idan ana son gyara Najeriya, sai mun gyara wasu sassa na aikinta ta hanyar raba masu hakar gwal da masu nacin mulki daga masu son yin hidima, don cimma haka sai munyi waje da wadanda ba su iya aiki ba da masu son kansu.

Kara karanta wannan

Shekarau: Dalilin Da Ya Sa Na Shiga Motar Gwamna Ganduje

"Amma, a wannan halin mai wuya, mun samo jajirtaccen dan siyasa a majalisar wakilai wanda ya san kallubalen shugabancin majalisar Najeriya. Shine Rt. Hon Muktar Aliyu Betara, mamba mai wakiltar Biu/Bayo/Shwa da Kwaya na Jihar Borno a Majalisar Tarayya."

Kwankwaso ne zai gaji Buhari, In Ji Bashir El-Rufai

Bashir El-Rufai, daya cikin yayan gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce Rabiu Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na NNPP a zaben 2023 ne zai zama 'magajin Shugaba Muhammadu Buhari.'

Bashir ya ce masu yi wa Kwankwaso dariya za su sha mamaki a nan gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164