Tashin Hankali Yayin Da Aka Bude Wa Tsohon Kwamishinan Ambode Da Wasu Wuta Yayin Kamfe Na LP A Legas

Tashin Hankali Yayin Da Aka Bude Wa Tsohon Kwamishinan Ambode Da Wasu Wuta Yayin Kamfe Na LP A Legas

  • Rikici ya barke yayin kamfe din jam'iyyar Labour a jihar Legas gabanin zaben ranar Asabar 18 ga watan Maris
  • Tsohon kwamishina karkashin gwamnatin tsohon Gwamna Ambode, Olawale Oluwo, na wurin kamfe din ya ce an harbe su amma sun sha da kyar
  • Dan takarar gwamna na jam'iyyar Labour a Legas, Gbadebo Rhodes-Vivour, shima ya tabbatar da harin amma ya ci kamfe din ta yi nasara

Epe, Jihar Legas - Tsohon kwamishina karkashin gwamnatin tsohon Gwamna Akinwunmi Ambode a Legas, Olawale Oluwo, ya ce an harbe su yayin kamfe din dan takarar gwamna na jam'iyyar Labour, Gbadebo Rhodes-Vivour a karamar hukumar Epe.

Daily Trust ta rahoto cewa Oluwo, amma, ya ce ya tsira ba tare da rauni ba.

Kamfe din LP
An rahoto yan saba sun kai hari yayin kamfe din LP a Legas. Hoto: @GRVlagos
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Zaben Gwamnan Ogun: Jam’iyyun Siyasa 10 Da Mambobin APC Sun Yi Maja Da PDP Don Tsige Gwamnan APC Daga Mulki

Legit.ng ta tattaro cewa Oluwo, dan takarar gwamna na jam'iyyar Boot a zaben gwamnan na ranar 18 ga watan Maris ya goyi bayan jam'iyyar Labour.

Yana tare da jigon PDP, Noheem Balogun, da wasu jiga-jigan jam'iyyar yayin kamfe din.

An tattaro cewa Ambode wanda ya rasa nasarar zarcewa a 2019 karkashin APC a yanzu yana goyon bayan dan takarar LP, Rhodes-Vivour.

Yadda harin ya faru - Oluwo

Da ya ke magana kan harin a ranar Asabar, 11 ga watan Maris, Oluwo ya ce lamarin ya faru a Ita Opo a Legas yayin kamfe din LP.

Ya ce duk da harin, an karasa kamfe din lafiya.

"An harbi Hon Noheem Balogun da ni, yau a Ita-Opo na Epe yayin da muke jagorantar kamfe din gwamna mai jiran gado na Legas (da izinin Allah), Mr Gbadebo Rhodes-Vivour," in ji shi.

Gbadebo Rhodes-Vivour ya tabbatar da harin

Dan takarar gwamna na LP a Legas, Rhodes-Vivour, shima ya tabbatar da harin a shafinsa na Twitter.

Kara karanta wannan

Bago VS Kantigi: Muhimman Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Manyan Yan Takara 2 a Jihar Neja

Ya rubuta:

"Ralli din jiya ta yi kyau, mun sada da mutane mun ga magoya baya a Epe. An kai mana hari amma dukkan mu lafiyan mu kalau. Abin kunya ne yadda wasu ke amfani da rikici don tsorata mu da ke son Legas mai kyau kuma bai dace a rika irin hakan a Legas ba. Ba za mu tsorata ba."

Nasiru Yusuf Gawuna: Abubuwa 10 Da Ya Kamata Ku Sani Kan Dan Takarar Gwamnan Kano Na APC

Dr Nasiru Yusuf Gawuna shine mataimakin gwamnan Jihar Kano kuma dan takarar gwamna na jam'iyyar APC da ke fatan darewa kan kujerar mai gidansa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Gawuna ya taba rike mukamin kwamishinan noma na jihar Kano kuma ya yi aiki da gwamnatoci uku a Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164