"Babban Nasara Ga APC" Gwamna Dapo Abiodun Ya Ce LP Ta Dawo Bayansa

"Babban Nasara Ga APC" Gwamna Dapo Abiodun Ya Ce LP Ta Dawo Bayansa

  • Gwamnan Ogun ya ce shugabanni da mambobin kwamitin zartaswa sun mara wa kudirinsa na neman tazarce baya
  • Dapo Abiodun na ɗaya daga cikin gwamnonin APC da ke fafutukar neman tazarce kan kujerunsu a zaben gwamnoni
  • Bayan tsaikon da aka samu, ranar 18 ga watan Maris, 2023, 'yan Najeriya zasu fita zaben gwamnoni a Najeriya

Ogun - Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, ya ce shugabannin jam'iyyar Labour Party na jihar sun amince zasu mara masa baya a zaben gwamnan da ke tafe.

Legit.ng Hausa ta rahoto cewa gwamna Abiodun na neman tazarce kan kujerarsa zango na biyu a zaben ranar 18 ga watan Maris, 2023.

Tawagar LP da gwamnan Ogun.
Gwamna Abiodun da shugabannin LP Hoto: @dabiodunMFR
Asali: Twitter

A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Tuwita ranar Jumu'a, gwamnan ya ce wannan ci gaban babban nasara ce ga jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Kara karanta wannan

Muhimman Abubuwa 10 Game Da Nasiru Yusuf Gawuna Dan Takarar Gwamnan Kano Na APC

Ya ce goyon baya daga tsagin jam'iyyar adawa wata babbar alama ce da ke nuna yadda tsaruka da shirye-shiryen da gwamnatinsa ta zo da su suka daɗaɗa wa kowa a jihar, har da jam'iyyun adawa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Mambobin kwamitin zartaswa da shugabannin LP a jihar Ogun sun goyi bayan kudirunmu na neman tazarce. Wannan babban nasara ce gare mu da jam'iyar mu ta APC mai albarka."
"Wannan goyon baya daga shugabannin jam'iyyar adawa na sahun gaba alama ce ta zahiri da ke nuna yadda ayyuka, da tsarun gwamnatin mu suka gyara Ogun kuma mutane sun gamsu."
"Ba zamu zama masu butulci da wannan nasara da Allah ya bamu ba, zamu ci gaba da faɗaɗa ayyukan mu da suka karɓu da kuma jawo kowa a jiki a harkar shugabanci."

- Dapo Abiodun.

A ranar Talata da ta gabata, shugaban LP na ƙasa, Julius Abure, ya ce jam'iyya ba ta umarci kowane reshe ya kulla alaƙa ko goyon bayan 'yan takarar wasu jam'iyyu ba.

Kara karanta wannan

DSS Ta Kama Mambobin Jam'iyyar PDP 3 A Kaduna 'Kan Shirin Tada Rikici' Yayin Zaben Gwamna Da Majalisun Jiha

Ina nan daram a PDP - Babangida Aliyu

A wani labarin kuma Tsohon Gwamnan Neja, Babangida Aliyu, Ya Musanta Koma Wa Jam'iyyar APC

Muazu Babangida Aliyu, tsohon gwamnan jihar Neja ya ce yana nan a jam'iyyar PDP, labarin da ake yaɗawa ya koma APC duk ƙanzon kurege ce.

Ya ce ya kammala duk wasu shirye-shirye don tabbatar da nasarar PDP a zaben gwamnoni da mambobin majalisar dokoki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262