Tsohon Gwamnan Neja, Babangida Aliyu, Ya Musanta Koma Wa APC

Tsohon Gwamnan Neja, Babangida Aliyu, Ya Musanta Koma Wa APC

  • Yayin da ake tsaka da yaɗa jita-jitar tsohon gwamnan Neja ya koma APC, ya fito ya karyata labarin baki ɗaya
  • Mu'azu Babangida Aliyu ya gargaɗi waɗanda suka ƙagi rahoton da su yi taka tsantsan kuma ya roki mutane su yi watsi da lamarin
  • Ya ce ya gama shiryawa tsaf domin aiki ba kama hannun yaro don tabbatar da nasarar PDP a zabe na gaba

Niger - Tsohon gwamnan jihar Neja, Mu'azu Babangida Aliyu, ya musanta jita-jitar da ake yaɗa wa cewa ya sauya sheka zuwa All Progressives Congress watau APC.

Jaridar Vanguard ta rahoto tsohon gwamnan ya ayyana jita-jitar da ƙarya wacce ba bu kamshin gaskiya a cikinta.

Muazu Babangida Aliyu.
Tsohon Gwamnan Neja, Babangida Aliyu, Ya Musanta Koma Wa APC Hoto: vanguard
Asali: UGC

A cewar Babagida Aliyu, har yanzun yana nan daram bai fita daga jam'iyyar PDP ba, saboda haka mutane su yi fatali da raɗe-raɗin wanda ya mamaye kafafen sada zumunta.

Kara karanta wannan

Mun kadu: Atiku da Tinubu sun yi gamin baki, sun yi jajen hadarin da ya faru a Legas

Tsohon gwamnan ya yi wannan karin haske kan labarin sauya shekarsa a wata sanarwa da ya fitar ta hannun hadiminsa, Prince Innocent Kure, a Minna, babban birnin Neja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan martanin na Babangida Aliyu ya zo ne daidai lokacin da ake tsaka da yaɗa jita-jitar ya tattara kayansa daga PDP ya koma APC a jihar da ke arewa ta tsakiya.

Ya jaddada cewa yana nan daram a matsayin cikakken mamba mai biyayya ga jam'iyyar PDP a matakin jiha da kuma ƙasa, kamar yadda rahoton Daily Post ya tabbatar.

Tsohon gwamnan ya yi bayanin cewa ya kammala shiri tsaf domin aikin tabbatar da nasarar PDP a zaben gwamna da mambobin majalisar dokoki da ke tafe ranar Asabar.

Babangida Aliyu ya ce:

"Irin wannan bayanan da ake yaɗawa karya ne kuma babu kamshin gaskiya a ciki, ya kamata mutane su ɗauke hankalinsu a kai musamman magoya bayan PDP."

Kara karanta wannan

An Gano Wanda Ya Haddasa Jirgin Kasa Ya Murkushe Motar Ma'aikatan Gwamnati a Legas

Bugu da ƙari, babban jigon siyasan ya gargaɗi duk masu hannu a kirkirar karyan da su shiga taitayinsu. Ya kuma bukaci masu katin zaɓe su fito su zaɓi PDP sak a zabe na gaba.

Yan daba sun kaiwa ayarin ɗan takara hari a Kaduna

A wani labarin kuma Yan Daba Sun Faramaki Ayarin Dan Takarar Gwamna a jahar Kaduna

Hadimin ɗan takarar gwamna, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce maharan sun raunata mutane hudu daga cikin tawagarsu, biyu maza biyu mata.

A cewarsa, jami'an tsaron da ke cikin ayarin ne suka shiga tsakani suka dakile yunƙurim 'yan daban.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262