Tsohon Dan Majalisa da Wasu Mambobin PDP Sun Sauya Sheka zuwa APC
- Jiga-jigai da mambobin jam'iyyar PDP sun sauya sheka zuwa APC mai mulki a jihar Ondo
- Jagoran tawagar masu sauya shekar kuma tsohon ɗan majalisa ya ce sun bar PDP ne saboda rigimar cikin gida
- Shugaban APC na jiha, Ade Adetimehin, ya ce ya fi kowa farin ciki da wannan matakin na kusoshin siyasa
Ondo - Kusan mako biyu bayan zaben shugaban kasa, wasu mambobi da jiga-jigan Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Ondo sun sauya sheƙa zuwa APC mai mulki ranar Alhamis.
Punch ta tattaro cewa masu sauya sheƙar sun fito daga kananan hukumomi 18 da ke faɗin jihar Ondo, kudu maso yammacin Najeriya.
Shugabannin jam'iyyar APC na jihar sun tarbe su hannu bibbiyu a sakatariyar jam'iyya da ke gefen Titin Oyemekun, Akure babban birnin Ondo.
Jagoran tawagar masu sauya sheƙar kuma tsohon mamba a majalisar dokokin jiha, Adeyinka Banso, ya ce sun fice daga PDP ne saboda rigingimun da suka mamaye ta.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya yi bayanin cewa ya dawo daga rakiyar jam'iyyar tun lokacin da ta tsayar da ɗan takarar shugaban kasa daga arewacin Najeriya. Ya ce hakan ya saɓa wa yarjejeniyar da aka yi a PDP.
A kalamansa ya ce:
"Mun zo nan ne mu tabbatar da mubaya'ar mu ga APC, muna goyon bayan shugaban mu kuma gwamna, Arakunrin Oluwarotimi Akeredolu, SAN, da shugaban jam'iyya, Jagaban Ondo, Ade Adetimehin."
"Mun shiga jam'iyyar ci gaba, idan na zauna a PDP ba zan samu damar wakiltar jama'ata ba har na yi abinda zai amfane su. Amma shigowa ta APC na ji na samu nutsuwa."
Da yake karban tsoffin jiga-jigan PDP da suka sauya sheƙa, shugaban APC na jihar, Ade Adetimehin, ya nuna farin cikinsa da wannan ci gaba. Ya ce kafin yanzu masu sauya sheƙar kusoshi ne a PDP.
Ya ce:
"Na fi kowa farin ciki yau, waɗan nan ne masu girgiza siyasar Ondo kuma su motsa ta. Asalin siyasa ita ce daga tushe, waɗan nan ne tushen siyasa."
Dan Takararmu Na Gwamna a Jihar Katsina Bai Janye Ba, Inji PDP
A wani labarin kuma Jam'iyyar PDP ta musanta wasikar da ke yawo cewa Yakubu Lado ya janye daga takarar gwamna Katsina
Kwamitin yakin neman zaben PDP a jihar Katsina ya ce jita-jitar ƙarya ce da bata yi kama da gaskiya ba, ya bayyana masu hannu a kitsa lamarin.
Asali: Legit.ng