“Wasu Na Shirin Haddasa Rikici Bayan Zaben Gwamnoni”, DSS Ta Gargadi Yan Najeriya
- Rundunar tsaron farin kaya ta gano kulla-kullan da wasu yan siyasa ke yi bayan zaben gwamnoni mai zuwa
- DSS ta ce wasu yan siyasa na shirin haddasa rikici a kasar idan har nasarar zaben bai zo bangarensu
- Hukumar tsaron ta kuma gargadi yan Najeriya musamman matasa da su guji rikici a zabe mai zuwa tare da bin doka
Abuja - Rundunar tsaron farin kaya ta DSS ta ce akwai tsare-tsare da ake yi na tayar da zaune tsaye a kasar nan.
Hukumar tsaron ta ce ana shirin aiwatar da makircin ne bayan zabukan gwamnoni da yan majalisun jihohi, rahoton The Cable.
A wata sanarwa da kakakin DSS, Peter Afunanya, ya saki a ranar Laraba, rundunar tsaron ta yi watsi da yadda ake kokarin haddasa zaman dardar a yankunan kasar.
Wani bangare na sanarwar na cewa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"An lura cewa wasu daga cikin masu assasa abun basa ga maciji da junansu. Lamarin na da hatsari sosai ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin kasar.
"A cikin haka ne hukumar ke gargadin yan siyasa da magoya bayansu da su yi aiki da hankali."
"Ana shawartan jama'a da su guji yada labaran karya, kalaman kiyayya da sauran kalamai da ka iya kawo karantsaye ga zaman lafiya. Bai kamata a dunga kallon siyada a matsayin abun a mutu ko ayi rai ba. Babu dalili da zai sa kowa ya dauki doka a hannunsa."
DSS ta bayar da shawara ga fusatattun yan siyasar Najeriya
Hukumar ta shawarci duk wanda ke ganin ba a kyauta masa ba da ya tafi kotu don neman gyara, yayin da ya yi kiraga mutane da su yi imani da tsarin.
Jaridar Vanguard ta kuma rahoto cewa DSS ta yi kira ga dukkanin yan Najeriya su zamo masu bin dokar zabe da tsare-tsarensa.
Yan bindiga sun farmaki garuruwan Neja, sun kashe mutum 6 da sace wasu 50
A wani labari na daban, mun ji cewa tsagerun yan bindiga sun kai kazamin hari kananan hukumomin Rafi da Wushishi da ke jihar Neja inda suka sace mutum 50 tare da halaka wasu shida.
Lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da ake shirye-shiryen zabukan gwamnoni da na yan majalisun jihohi a fadin kasar.
Asali: Legit.ng