Kwana Uku Gabanin Zabe, Kotu Ta Tsige Ɗan Takarar LP a Jihar Benuwai

Kwana Uku Gabanin Zabe, Kotu Ta Tsige Ɗan Takarar LP a Jihar Benuwai

  • Kwanaki kalilan gabanin zaben gwamnoni, babbar Kotun tarayya ta jiƙa wa jam'iyyar LP aiki a jihar Benuwai
  • Alkalin Kotun ya tunbuke ɗan takarar mataimakin gwamnan LP kana ya maye gurbinsa da wani sabo
  • Labour Party na ɗaya daga cikin manyan jam'iyyun da ake hasashen zasu iya lashe kujerar gwamnan a jihar Benuwai

Abuja - Babbar Kotun tarayya mai zama a Abuja ta soke tikitin ɗan takarar mataimakin gwamna na jam'iyyar Labour Party a jihar Benuwai, Idu Onyiloyi.

Kotun karkashin jagorancin mai shari'a Inyang Ekwo, ta maida Ochechi Adejor a matsayin ɗan takarar mataimakin gwamnan Benuwai a inuwar LP, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Labour Party.
Magiya bayan LP kenan yayin da suka fito tattakin goyon bayan Peter Obi a Abuja
Asali: Getty Images

Da yake yanke hukunci kan ƙarar da Adejor ya shigar, Alkalin Kotun ya ce tun da Onyiloyi ya janye daga takarar gwamna bisa raɗin kansa babu ta yadda zai dawo kan matsayin daga baya.

Kara karanta wannan

Ta Kwaɓe, Yar Takarar Mataimakin Gwamna Ta Yi Murabus, Ta Koma APC da Dubbannin Mambobi

Mai shari'a Ekwo ya ce ya gamsu da bayanin cewa Mista Onyiloyi da karan kansa ya rubuta takardar murabus daga takara kuma ya haɗa ta da umarnin Kotu kana ya tura wa LP.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dogaro da sashi na 221, 222, na kundin mulkin Najeriya da sashi na 29, 31, 32, 33 da 84 na kundin dokokin zaɓe 2022, Alkalin Kotun ya ce ya zama tilas jam'iyar ta cire Onyiloyi ta maye gurbinsa da Adejor.

Punch tace Ekwo ya umarci jam'iyyar Labour Party ta gaggauta tura sunan Adejor zuwa ga hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) domin sanya shi a matsayin halastaccen ɗan takarar mataimakin gwamna.

Bugu da ƙari, Alƙalin Kotun ya umarci Mista Onyiloyi ya daina nuna kansa a matsayin ɗan takarar mataimakin gwamna na LP a jihar Benuwai.

Haka nan ya haramtawa ita kanta jam'iyyar LP ci gaba da ayyana shi a matsayin abokin takarar mai neman kujerar gwamna.

Kara karanta wannan

Muna Jiran Hukuncin Kotun ƙoli Akan Lamarin Shekarau Inji NNPP

INEC ta yi nasara kan bukatar Obi

A wani labarin kuma Kotu Ta Amince Wa INEC Ta goge Na'urar BVAS, Ta Yi Watsi da Bukatar Obi

Kotun ɗaukaka kara ta sahalewa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta sake saita na'urorin BVAS domin shirya wa zaben gwamnoni mai zuwa.

Hakan ya biyo bayan wani bayani da INEC ta yi a zaman Kotun wanda mai kara, Peter Obi, bai yi musu ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262