Shawarar da na ba Atiku a kan yadda za a shawo kan rigingimun PDP – Ayo Fayose

Shawarar da na ba Atiku a kan yadda za a shawo kan rigingimun PDP – Ayo Fayose

  • Ayodele Fayose ya shaida cewa ya ba Atiku Abubakar shawara a kan hanyoyin dinke barakar PDP
  • Tsohon Gwamnan jihar Ekiti ya nuna mutanen da ke zagaye da ‘dan takaran ba su dauki shawararsa ba
  • Fayose ya ce ya zauna da ‘Dan takaransu a otel, ya roke shi ya amince da bukatar Gwamnonin G5

Lagos - Tsohon Gwamna a Ekiti, Ayodele Fayose ya ce ya bada shawara ga Atiku Abubakar da ya nemi takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyar PDP.

Da aka zanta da shi a tashar talabijin TVC a ranar Laraba, Ayo Fayose ya ce ya ba ‘dan takarar shawarar yadda za a magance rigimar cikin gidan jam’iyya.

Mutanen da ke kusa da Wazirin Adamawa sun yi ta nunawa Fayose ba za a karbi maganarsa ba, su na cewa Atiku ba zai yarda ya kunyata kansa ba.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari Ya Fayyace Komai Bayan An Ga Babu Sunansa Cikin Lauyoyin Tinubu

“Oga ba zai yarda da wannan ba”

A tattaunawar da aka yi da shi, Fayose ya ce ya fadawa Atiku ya ziyarci Fatakwal su hadu da Gwamna Nyesom Wike, amma aka yi watsi da shawarar.

‘Dan siyasar ya ce ya samu Atiku a otel, ya fada masa yana so PDP ta ci zabe, ya jero masa bukatun G5, sai aka dage cewa ba za a iya cire Iyorchia Ayu ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Gangamin PDP
Gangamin PDP a Uyo Hoto: www.bbc.com
Asali: UGC

Fayose zai bar PDP?

Mista Fayose ya yi karin haske a kan jita-jitar ficewarsa daga jam’iyyar PDP, ya ce duk da yana ganin darajar Bola Tinubu, ba zai taba shiga APC ba.

‘Dan siyasar ya nuna har gobe yana nan a PDP kuma yana rike da mukamai, amma yake cewa idan ana batun kishin Najeriya, ba a kawo wata jam’iyya.

Kara karanta wannan

INEC ta Bada Dalilin Cire Sunan Yaron Tsohon Gwamna Cikin Zababbun ‘Yan Majalisa

“Akwai bukatar a samu wanda zai rika fadan gaskiya ba tare da shiga rigar jam’iyya ba.

- Ayo Fayose

A ra’ayin Fayose wanda ya yi Gwamna a Ekiti sau biyu, ba ayi magudi a zaben shugaban kasa ba, yana ganin Asiwaju Bola Tinubu ya yi galaba.

Vanguard ta rahoto tsohon shugaban kungiyar Gwamnonin na PDP yana yabon Peter Obi, amma ya ce a zabi jam’iyyar PDP a matakin zaben Jihohi.

Wike da kungiyar G5

A baya an ji labari cewa jagora a jam'iyyar PDP, Murtala Adamu Kimba ya yi bayanin dalilin rashin nasarar jam'iyyar PDP a zaben shugaban kasa.

Murtala Adamu Kimba ya ce Gwamna Wike ya yi tunanin zai samu takarar mataimakin shugaban kasa a 2023, amma bai yi nasara ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng