2023: INEC Ta Soke Zabe a Mazabar Shugaban Masu Rinjaye, Ado Doguwa
- Hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta soke sakamakon zaben da ta bayyana a mazabar Doguwa/Tudun Wada da ke Kano
- Farfesa Ibrahim Yakasai, baturen zabe ya ce sun sake nazari kan sakamkon kuma sun gano akwai tufka da warwara
- Bisa haka ya ayyana zabe a matsayin wanda bai kammalu ba kuma INEC zata shirya zabe a wasu rumfuna 13
Kano - Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta soke zabe a rumfuna 13 da ke mazaɓar ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Doguwa/Tudun Wada, Al-Hasaan Ado Diguwa.
Baturan zabe mai alhakin tattara sakamako a mazaɓar, Farfesa Ibrahim Yakasai, ya ce tursasa shi akai ya ayyana wanda ya samu nasara a baya.
Da yake jawabi a hedkwatar INEC, Farfesa Yakasai ya ce an soke zabe a rumfuna 13 da ke yankin karamar hukumar Doguwa kuma adadin masu kaɗa kuri'a sun zarce tazarar da ke tsakanin NNPP da APC.
Bisa haka ya ce INEC zata sake sanya lokaci ta gudanar da zaɓe a rumfunan da lamarin ya shafa kafin ayyana halastaccen wanda ya lashe zaɓe a mazaɓar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Meyasa INEC ta soke sakamakon?
Da yake jawabi a wani bidiyo da Daily Trust ta wallafa a Tuwita, Yakasai ya ce kundin dokokin zabe sun ba INEC dama ta sake nazari kan sakamkon da ta riga da ta bayyana.
A cikin kalamansa, Yakasai ya ce:
"INEC ta yi amfani da tanadin doka ta sake nazari kan sakamakon zaben da ya gudana a mazaɓar wanda ya nuna, APC ta samu kuri'u 39, 732 yayin da NNPP ke mara mata baya da kuri'u 34, 798."
"Haka nan an soke zaɓe a rumfuna 13, kuma mutane 7,083 ne suka yi rijista yayin da 6,917 suka karbi katin zaɓensu a waɗan nan rumfuna. Tazarar da ke tsakanin APC da NNPP 4,934."
A cewarsa, idan aka haɗa kuri'un NNPP da na mutanen dake da katin zaɓe a rumfuna 13 da aka soke zata haura APC, "Bisa haka INEC zata sa lokaci a sake zaɓe a rumfunan don tantance wanda ya samu nasara."
Gwamna Wike Ya Karbi Masu Sauya Sheka Daga APC Zuwa PDP a Ribas
A wani labarin kuma Gwamna Wike Ya Ƙara Rikita Lissafin APC Ana Dab da Zaben Gwamnoni a Najeriya
Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya yi maraba da wasu jiga-jigai da mambobin APC waɗanda suka yanke sauya sheka zuwa PDP a Ribas.
Wike wanda ya halarci wurin karban yan siyasan a ƙaramar hukumar Ahoada ta gabas ya ɗauki sabbin alƙawurra.
Asali: Legit.ng