"Zan Tattauna Da Ƴan Bindiga Idan Aka Zaɓe Ni" Ɗan Takarar Gwamnan PDP a Kaduna

"Zan Tattauna Da Ƴan Bindiga Idan Aka Zaɓe Ni" Ɗan Takarar Gwamnan PDP a Kaduna

  • Ɗan takarar gwamnan jihar Kaduna a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), yayi tsokaci kan matsalar tsaron jihar
  • Isah Ashiru Kudan ya bayyana cewa da zarar ya hau mulki zai rungumi matakin sulhu da ƴan bindiga domin kawo ƙarshen matsalar tsaro a jihar
  • Ɗan takarar yace ƴan bindigan mutane ne kamar kowa saboda haka yana da kyau a zauna da su domin a fahimci matsalolin su

Kaduna- Ɗan takarar gwamnan jihar Kaduna a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Isah Ashiru Kudan, ya bayyana hanyoyin da zai bi domin magance matsalar ƴan bindiga a jihar.

Ashiru Kudan ya bayyana cewa domin shawo kan matsalar, gwamnatin sa zata tattauna da ɓata garin domin samun maslaha inda yayi nuni da cewa su ma mutane ne ba dodanni ba. Rahoton Daily Trust

Kara karanta wannan

Bayan Ya Garzaya Kotu, Peter Obi Ya Aikewa Magoya Bayansa Da Wani Muhimmin Gargaɗi

Kudan
"Zan Tattauna Da Ƴan Bindiga Idan Aka Zaɓe Ni" Ɗan Takarar Gwamnan PDP a Kaduna Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Kudan ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da tashar talabijin ta ARISE TV, kan batutuwan da suka shafi nasarar jam'iyyar sa a zaɓen gwamna na dan ƴan majalisun jihar na ranar 11 ga watan Maris, 2023.

Ɗan takarar na jam'iyyar PDP, ya soki wasu shirye-shirye na gwamnatin Malam Nasiru El-Rufai, ciki harda korar wasu sarakunan gargajiya, inda ya ƙara da cewa hakan ya taimaka wajen ƙara taɓarɓarewar tsaro a jihar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A kalamansa:

“Maganar gaskiya itace ko muna so ko bamu so, dole sai mun sanya mutane wajen ganin mun shawo kan wannan matsalar tsaron."
"Dole ne mu zauna da mutanen nan masu garkuwa da mutane. Mutane ne masu rayuwa a cikin mu. Mutane na tunanin cewa dodanni ne, ba haka bane. Zamu iya zama da su, mu tattauna da su, sannan mu kawo ƙarshen wannan masifar."

Kara karanta wannan

Abubuwa 6 Da Ya Wajaba Tinubu Tunkara Gadan-Gadan a Matsayin Shugaban Ƙasa

“Matsalar dake a Kaduna abin tashin hankali ne. Zo Kaduna ka gani. Mutane basu iya barci cikin kwanciyar hankali"
"Idan har muna son mu kawo ƙarshen wannan ta'adancin a cikin al'ummar mu, dole ne a zauna da mutanen nan domin tabbatar da cewa duk wata matsalar su an magance ta.

Zaɓen Gwamnoni: Jam'iyyar Labour Party Ta Musanta Haɗewa Da PDP a Jihar Kaduna

A wani labarin na daban kuma, jam'iyyar Labour Party ta musanta narkewa cikin jam'iyyar PDP a jihar Kaduna.

Jam'iyyar ta bayyana cewa ko kaɗan va zata taɓa haɗewa da PDP ba ko wata jam'iyyar a jihar Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng