“Sai Da Na Roki Allah Ya Sa Tinubu Ya Ci Zabe”, Inji Gwamna Umahi
- Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi ya magantu kan yadda ya dukufa wajen rokawa yan takarar APC nasara a zaben 2023
- Umahi ya ce sai da ya dage wajen rokon Allah ya sa Bola Tinubu ya lashe zaben shugaban kasa
- Zababben sanatan ya kuma yi kira ga al'ummar Ibo da su marawa gwamnati baya don ci gabansu
Ebonyi - Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ya ce ya dage wajen addu'a kan Allah ya sa zababben shgugaban kasa, Bola Tinubu ya yi nasara a zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu.
Umahi ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 7 ga watan Fabrairu, a Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi, yayin da yake jawabi ga masu ruwa da tsaki da mutanen kabilar Izzi, rahoton The Cable.
Sabon Harin Zamfara Da Kano: Tinubu Ya Yi Allah Wadai, Ya Ce Dole a Takawa Kashe-Kashe Birki a Najeriya
Gwamnan ya ce bai boye addu'o'insa ga Allah ba cewa Tinubu da dukkanin yan takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) su lashe zaben.
Ya ce:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Na roki Allah ya kawo Tinubu kan mulki, ya bani muryar tsayawa da mutanen da kuma kawo hadin kai a Najeriya.
"Na yi wa Allah alkawarin cewa zan yi gwagwarmaya don hada kan kasar nan da kawo zaman lafiya da wadata a cikinta.
"Wannan shine alkawarin da na yi wa Allah kuma zan aikata hakan saboda lokaci ya yi da shugabannin kasar nan za su sadaukar da abubuwa.
"Yanayin ya yi muni, albarkatun kasar nan za su iya bunkasa shi, inda Ebonyi za ta zamo abun kwatance."
Ku marawa gwamnati baya, Umahi ga kabilar Ibo
Umahi ya yi kira ga al'ummar Ibo da su marawa gwamnati baya a jihohinsu mabanbanta don su samu zaman lafiya, rahoton Vanguard.
"A inda mutum yake zaune ne yake ci gaba kasancewar ba ku iya zama a wuri sannan ku shiryawa mutanensa munakisa ba."
Gwamnan ya kuma bukaci mutanen Izzi da su hada kai don lashe zaben gwamna.
"Ba zan marawa wani daga yankin kudancin jihar ya zama magajina ba," cewarsa.
"Duk dan Izzi da ke goyon bayan wani daga kudu don zama gwamna bai da tunani amma fada ku yaki wannan mutumin.
"Wannan mutumin ya rigada ya illata kansa saboda yanzu lokacin mayar maku da alkhairi ne kan goyon bayan kudu a 2015."
Umahi shine zababben sanata mai wakiltan yankin Ebonyi ta kudu.
A wani labari na daban, Festus Keyamo ya yi bayani cewa ba zai iya shiga tawagar lauyoyin Bola Tinubu ba a kotun zabe saboda shi minista ne mai ci a gwamnatin Shugaba Buhari.
Asali: Legit.ng