"PDP Zata Ja Jihohi 15, APC 10” - EiE, SBM Sun Yi Hasashen Yadda Zaben Gwamna Za Ta Kasance
Gabannin zabukan gwamnoni na ranar 11 ga watan Maris kungiyoyin leken asiri na Enough is Enough (EiE) da SB Morgen (SBM) sun saki sakamakon binciken da suka gudanar don gano wadanda ka iya lashe zaben.
Za a gudanar da zabukan gwamnoni a fadin jihohi 28 cikin 36 na kasar Najeriya.
A wani rahoto mai taken: "Hasashen zabe na EiE-SBM: Tseren gwamnoni', kungiyoyin sun yi hasashen jihohin da jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki, Peoples Democratic Party (PDP) da sauransu za su iya lashewa.
Rahoton ya ce mutane 8,921 aka yi wa tambayoyi game da tseren zabukan shugaban kasa, gwamnoni da na yan majalisu tsakanin 16 ga watan Janairu zuwa 3 ga watan Fabrairun 2023.
Kungiyoyin sun kuma yi wa mutane 2,613 tambayoyi ta kan wayar tarho a fadin jihohi 36 da Abuja.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sai dai kuma, amsoshin da aka samu daga binciken jama'ar gari kawai aka yi amfani da su wajen hasashen yadda zabukan gwamnonin za su kasance.
Sakamakon bincikensu ya nuna PDP a gaba inda aka yi hasashen cewa babbar jam'iyyar adawar ce za ta lashe jihohi 15 yayin da APC za ta tashi da 10.
An yi hasashen cewa jam'iyyar Labour Party za ta lashe jiha daya. Kalli cikakken sakamakon a kasa:
Jihohin da APC za ta iya lashewa
- Borno
- Yobe
- Jigawa
- Zamfara
- Niger
- Kwara
- Nasarawa
- Benue
- Ogun
- Lagos
Jihohin da PDP za ta iya lashewa
- Sokoto
- Kebbi
- Oyo
- Katsina
- Kaduna
- Bauchi
- Gombe
- Adamawa
- Cross River
- Akwa Ibom
- Rivers
- Delta
- Taraba
- Ebonyi
- Plateau
Yanzu Yanzu: Tashin Hankali Yayin da Jam’iyyun Siyasa 4 Ke Shirin Maja Don Tsige Gwamnan APC a Wata Jihar Arewa
Jihar da Labour Party za ta iya lashewa
- Abia
Jihar da NNPP za ta iya lashewa
- Kano
Jihar da APGA za ta iya kawowa
- Enugu
Jam'iyyar PDP ta zargi INEC da yunkuri goge shaidar magudi a zaben shugaban kasa na 2023
A wani labari na daban, mun ji cewa jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta yi zargin cewa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta na yunkurin goge shaidun da ke tabbatar da an yi magudi a zaben shugaban kasa na 2023.
PDP ta ce hukumar INEC na kokarin goge bayanan da ke kunshe a cikin na'urorin BVAS da sunan sake saita su gabannin zaben gwamnoni.
Asali: Legit.ng