Gwamna Wike Ya Karbi Masu Sauya Sheka Daga APC Zuwa PDP a Ribas
- Gwamna Wike na jihar Ribas ya kara durkusad da jam'iyyar APC yayin da ake dab a zaben gwamna ranar Asabar
- A ranar Talata 7 ga watan Maris, Wike ya karbi wasu gungun mambobin APC da suka sauya sheka zuwa PDP
- A cewar jagoran tawagar yan siyasan, sun zabi shiga PDP ne domin jawo wa yankinsu ayyukan ci gaba
Rivers - Gwamnan Ribas, Nyesom Wike, ya jaddada cewa babu tantama Peoples Democratic Party (PDP) ce zata lashe zaben gwamna da mambobin majalisar dokokin jihar.
Wike ya yi wannan furucin ne ranar Talata yayin da yake karɓan dandazon mambobin APC da suka sauya sheka zuwa PDP a ƙaramar hukumar Ahoada ta gabas.
Channels tv ta tattaro tsoffin mambobin jam'iyyar APC sun ɗauki wannan mataki ne bisa jagorancin tsohon ɗan takarar majalisar tarayya a yankin, Eric Apia.
A wurin taron shagalin da aka shirya a garin Ehuda clan, mahaifar jagoran masu sauya sheƙar, gwamna Wike ya yi alƙawarin gina Titi mai tsawon kilomita 10 a cikin gari.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Haka nan kuma Wike ya ba da kwangilan sabunta ginin makarantar Sakandiren matata gwamnati da ke garin Ahoada.
Meyasa suka zaɓi komawa PDP?
A nasa jawabin, Mista Apia, tsohon ɗan takarar majalisar wakilai a inuwar APC, ya ce ya zabi shiga PDP a dama da shi ne domin jawo ayyukan ci gaba da al'ummarsa.
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa wannan ci gaban ya zo ne awanni bayan shugabannin Labour Party a Ribas sun koma bayan ɗan takarar gwamnan PDP, Siminialayi Fubara.
Faruwar haka ke da wuya, uwar jam'iyyar LP ta kasa ta sanar da rushe kwamitin shugabannin jam'iyya na reshen Ribas sakamakon wannan mataki da suka ɗauka.
A ranar Asabar mai zuwa, 11 ga watan Maris, 2023 za'a fafata zaben gwamnoni a Najeriya kuma zai gudana a mafi akasarin jihohi.
Kotun Koli ta raba gardama a jihar Akwa Ibom
A wani labarin kuma Kotun Koli Ta Tabbatar da Nasarar Ɗan Takarar Gwamnan APC a Akwa Ibom
Yayin yanke hukunci ranar Talata, kwamitin Alkalai biyar ya bayyana cewa Mista Udofia ne halastaccen ɗan takarar gwamna a inuwar APC.
Alkalan sun ce zargin da ake cewa ɗan takarar bai zama cikakken mamban APC a lokacin zabenba ba gaskiya ba ne.
Asali: Legit.ng