“Mun Yi Allah Wadai Da Belin Ado Doguwa”, Inji Kwankwaso

“Mun Yi Allah Wadai Da Belin Ado Doguwa”, Inji Kwankwaso

  • Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi watsi da belin da kotu ta baiwa Alhassan Ado Doguwa
  • Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP a zaben 2023 da aka kammala ya ce yan sanda sun rubuta duk chaji da ake yi wa Doguwa amma aka sake shi
  • Kwankwaso ya ce rashin aiki da doka a Najeriya ita ce ta sa kasar ke inda take a yau

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi Allah wadai da belin da aka baiwa shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai, Alhassan Ado Doguwa.

A makon jiya ne dai yan sanda suka kama dan majalisar bisa zarginsa da ake da hannu a kisan kai da kona sakatariyar jam'iyyar NNPP a jihar Kano.'

Kara karanta wannan

Shin Kwankwaso Ya Taya Zababben Shugaban Kasa Bola Tinubu Murna, NNPP Ta Yi Karin Haske

Rabiu Musa Kwankwaso yana magana
Zargin Kisa: “Mun Yi Allah Wadai Da Belin Ado Doguwa”, Kwankwaso Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Yan sanda sun yi chaji mai kyau kan Doguwa amma aka sake shi, Kwankwaso

Kwankwaso ya bayyana cewa lauyoyinsu sun sanar da shi cewa jami'an yan sanda sun rubuta duk wasu hujjoji masu kyau a kan Doguwa amma kasancewar Najeriya ba doka sai ga shi an bayar da belinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin bidiyon wanda VOA Hausa ya wallafa a Facebook, an jiyo Kwankwaso na cewa:

“Kana ganin mutane a gashe an kone su abun tausayi, an babbake mutane, wadansu ga kabarurrukansu nan, wasu ga su nan harsashi dukka a jikinsu.
“Dan sandan ma da aka karbi bindigar a hannunsa aka yi harbin ance har yanzu yana tsare a hannun hukuma.
“Duk wannan shaidu duk an tattarasu, yan sanda ni ba mutumin yan sanda bane yawanci, amma dai a wannan karon labarin da na samu wajen lauyoyinmu sun yi chaji masu kyau wanda suke na gaskiya na abubuwan da jama’a suka fada mana na kashe ko harbe mutane, na babbake mutane, na kona kayan al’umma , na ta da tarzoma duk abun da wani chaji wanda yake aka yi shi a wajen babu wanda yan sanda basu rubuta ba.

Kara karanta wannan

Sabuwar Matsala Ta Bullo Yayin da Bankuna Suka Fara Zuba Tsoffin N500 da N1000 a ATM

“Toh amma ka gani da yake Najeriya kenan, Najeriya yau an wayi gari za ka dauki bindiga ka kashe mutane, ka dauki ashana ka kona guri, shikenan ka yi kwana biyu shikenan sai ace an sallame ka, ka tafi gida an baka beli. Wannan rashin hukunci shine ya kawo mu inda muke ciki a halin yanzu mu a ra’ayinmu a Najeriya.”

Ga bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Shehu Sabo Gashua ya yi martani:

"Belin Hon. Ado Doguwa da kotu ta bayar ya tabbatar mana cewa a Najeriya talaka ne kawai zai aikata laifi doka tayi aiki akansa."

Aminu Dan Almajiri ya ce:

"Allah ya kara shiga lamarin ka dan musa."

Amina Kabir Abubakar ta ce:

"Nigeria cefa Madugu, inda Dan takara bai sai form ba, bai tsaya takararba, amma ance shine winner. Aitayi, akwai lahira."

A wani labari na daban, gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya yi afuwa ga wasu fursunoni 12 da aka yankewa hukuncin kisa a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng