Kotun Koli Ta Tabbatar da Nasarar Ɗan Takarar Gwamnan APC a Akwa Ibom
- Kotu mai daraja ta ɗaya a Najeriya ta yanke hukuncin ƙarshe kan sahihin ɗan takarar APC a zaben gwamnan jihar Akwa Ibom
- A ranar Talata 7 ga watan Maris, 2023, Kotun koli ta tabbatar da ingancin takarar Mista Akan Udofia
- Tun farko Sanata Ita Enang ya roki Kotu ta karbe takara daga hannu Udofia ta ba shi saboda wasu dalilai da ya bayyana
Abuja - Kotun koli, a ranar Talata, ta tabbatar da Mista Akan Udofia, a matsayin halastaccen ɗan takarar gwamnan jihar Akwa Ibom na jam'iyyar APC.
Jaridar Premium Times ta tattaro cewa INEC ta shirya gudanar da zaben gwamnoni a Najeriya ranar 11 ga watan Maris, 2023.
Tsohon Sanata, Ita Enang, ne ya nemi Kotu ta rushe zaɓen Mista Akan a matsayin ɗan takarar gwamnan APC na jihar.
Enang ya roki Kotun ta ayyana shi a matsayin halastaccen ɗan takarar APC bisa hujjar cewa Mista Udofia bai zama cikakken mamban APC ba zuwa ranar 27 ga watan Mayu, 2022 lokacin da aka gudanar da zaben fidda gwani.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Amma yayin bayyana hukunci yau Talata, kwanitin alƙalan Kotun koli 5 karkashin jagorancin Kudirat Kekere-Ekun ta ce Mista Udofia ya zama mamban APC lokacin da aka gudanar da zaɓen.
Mai shari'a Kekere-Ekun ta ƙara da cewa kowace jam'iyyar siyasa na da ikon baiwa kowane mutum damar zama cikakken mamba.
Punch ta rahoto Alkalin ta ce:
"Ina goyon bayan karamar Kotu cewa wanda ake ƙara na farko, Mista Udofia, yana cikin inuwar APC sa'ilin da aka yi zaben fidda gwani kuma batun ɗauke sharadi wani abu ne na cikin gida da Kotu ba zata tsoma baki ba."
Bugu da ƙari, Alkalin ta ce kasancewar an tabbatar da sahihancin takarar Udofia, hakan ya nuna karara da Sanata Enang ya shigar da rushe.
APC da naɗa SAN 12 domin su kare nasarar Tinubu
A wani labarin kuma Jam'iyyar APC Ta Nada Manyan Lauyoyi 12 Da Zasu Kare Nasarar Tinubu a Kotu
A wata sanarwa da APC ta fitar a shafinta na Tuwita, ta bayyana sunayen mutane 12 da karin mai ba da shawara kan harkokin shari'a na APC ta ƙasa a matsayin na 13.
Wannan na zuwa ne yayin da Atiku da Peter Obi suka shigar kara gaban kotun sauraron korafe-korafen da suka shafi zaɓen shugaban kasa a Najeriya.
Asali: Legit.ng