Zababbun Sanatoci Sun Karbi Takardar Shaidar Cin Zabe Daga Wajen INEC a Abuja
- Yan majalisa da aka zabe a zaben majalisar dokokin tarayya da ya gudana a ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu sun karbi takardar shaidar cin zabensu
- Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ce ta gabatarwa yan majalisar da wadannan satifiket din
- An gabatarwa zababbun sanatocin da satifikets dinsu ne a cibiyar taro ta kasa da kasa da ke Abuja
Abuja - A ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu ne yan Najeriya suka je rumfunar zabe don zabar yan majalisar da za su wakilci mazabunsu a matakin kasa.
An ayyana wasu daga cikin sanatocin da aka zaba a matsayin wadanda suka lashe zabe nan take yayin da aka ayyana wadanda zabukan yankinsu bai kammalu ba daga baya.

Asali: Twitter
Wata wallafa da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta yi ya nuna cewa an mikawa zababbun sanatocin takardun shaidar cin zabensu a cibiyar kasa da kasa da ke Abuja a ranar Talata, 7 ga watan Maris.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Wasu daga cikin yan takarar da suka yi nasarar zuwa majalisar dattawa ta Goma sun hada da Orji Uzor-Kalu wanda ke wakiltan Abia ta kudu, da Ahmad Lawan wanda a yanzu haka shine shugaban majalisar dattawa ta tara. Lawan zai wakilci Yobe ta arewa.
Har ila yau, yayin da INEC ta saki jerin sunayen wadanda aka zaba a majalisar wakilai, ba a baiwa wadannan yan majalisar takardar shaidar cin zabensu ba.
INEC ta cire sunan Doguwa cikin zababbun yan majalisar wakilai
A gefe guda, mun ji cewa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta, INEC, ta cire sunan Alhassan Ado Doguwa na jihar Kano daga cikin wadanda suka yi nasara a zaben majalisar wakilai na 2023.
Da farko INEC ta ayyana Doguwa a matsayin wanda ya yi nasara a zabe sai dai kuma ko sama ko kasa ba a ga sunansa ba a cikin jerin sunayen zababbun yan majalisa da aka saki a ranar Talata.
Kamar yadda hukumar ta sanar, ta ce an matsawa baturen zaben yankin wajen ayyana Doguwa a matsayin wanda ya lashe zaben dan majalisar wakilai mai wakiltan mazabar Doguwa/Tudun Wada a jihar Kano.
Jam'iyyar PDP ta ce lallai Atiku ne ya ci zabe ba Tinubu ba
A wani labari na daban, jam'iyyar PDP ta yi watsi da ayyana Asiwaju Bola Tinubu a matsayin zababben shugaban kasa, ta ce lallai dan takararta, Atiku Abubakar ne ya ci zabe.
Asali: Legit.ng