Dino Melaye Ya Bayyana Adadin Biliyoyin da PDP Ta Kashe a Yakin Zaben Atiku Abubakar
- Mai magana da yawun kwamitin neman zaben shugaban kasa na PDP ya soki hukumar INEC
- Dino Melaye ya ce canjin kudi da aka fito da shi gabanin zabe ba komai ba ne face yaudara kurum
- Zargin da Sanata Melaye yake yi shi ne an rabawa Bola Tinubu sababbin kudi, an hana ‘Yan APC
Abuja - Babban mai magana da yawun bakin kwamitin yakin zaben Atiku-Okowa a jam’iyyar PDP, Dino Melaye ya yi magana a kan canjin kudi.
Punch ta ce Sanata Dino Melaye ya yi magana a wani bidiyo inda aka ji ya ce yaudarar jama’a aka yi a wajen canza N200, N500 da N1000.
Kakakin kwamitin kamfen na zaben 2023 ya ce an ba Bola Tinubu da ‘yan jam’iyyar APC sababbin kudi a ranar babban zabe, amma aka hana PDP.
A gajeren bidiyon, kakakin na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa a jam’iyyar PDP ya ce sun batar da sama da Naira biliyan 400.
INEC ta yaudari 'Yan Najeriya?
Sanata Melaye yake cewa sun kashe makudan kudin ne domin Atiku Abubakar ya samu nasara, amma a karshe ya ce INEC ta yaudari mutane.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Bayanin Dino Melaye ya zo ne bayan Dr. Iyorchia Ayu da sauran kusoshin jam’iyyar adawar sun yi zanga-zanga a hedikwatar INEC a kan zaben 2023.
"Domin a tabbatar da cewa an mikawa Atiku Abubakar mulki, mun kashe sama da Naira biliyan 400 saboda wannan shiririta, INEC ta yaudari ‘Yan kasa."
- Sanata Dino Melaye
Tsohon Sanatan na yammacin Kogi bai yi karin bayani a kan inda kudin kamfen su ka tafi ba.
Abin da doka ta ce a kan kamfe
A dokar zabe, ‘dan takaran shugaban kasa yana iya kashe abin da bai zarce Naira biliyan 5 ba, idan kudin ya wuce hakan, EFCC za ta iya kama shi.
Baya ga kudin da aka kashe wajen yakin neman zabe, bisa dukkan alamu jam’iyyar PDP ko Atiku Abubakar za su sake kashe miliyoyi a shari’ar zabe.
A lokacin da aka shiga kotun sauraron karar zabe a 2019, ana tunanin 'yan takaran APC da PDP sun kashe Naira biliyan 5, a karshe Atiku bai dace ba.
Meya jawo APC ta rasa wasu Jihohinta?
Ba a Legas kurum ba, kun ji labarin abin da ya jawo jam'iyyar APC ta fadi zabe a Nasarawa, Yobe, Gombe, Katsina, Filato, Imo, Kuros Riba da Ebonyi.
Abdullahi Adamu ya rasa Nasarawa, Gwamnoni irinsu Abdullahi Ganduje da Nasir El-Rufai ba su kawo jihohinsu ba, kuma PDP ta bada mamaki a Yobe.
Asali: Legit.ng