Malamai Sun Yi Wa Gwamna Addu'a Yayin da Mambobin PDP Suka Koma APC
- Malamai a yankin Okele da ke jihar Kwara sun shirya Addu'a ta musamman domin nasarar gwamna AbdulRazaq
- Wannan na zuwa ne jim kaɗan bayan wasu jiga-jigai da mambobin PDP 300 sun sauya sheka zuwa APC a yankin
- A cewar Malaman da suka halarci taron gwamna AbdulRazaq ya cancanci sake komawa kujerarsa a zango na biyu
Kwara - Malaman Addinin Musulunci a Okele, gundumar Ibagun da ke ƙaramar hukumar Ilorin ta gabas sun gudanar da taron addu'a na musamman domin rokon Allah ya baiwa gwamnan Kwara nasara.
Leadership ta rahoto cewa Malaman sun taru sun yi wa gwamna AbdulRahman AbdulRazaq addu'ar Allah ya ba shi nasarar zarcewa kan kujerarsa a zaben da ke tafe ranar Asabar.
Wannan ci gaban na zuwa ne jim kaɗan bayan mambobin jam'iyyar PDP 300 a yankin Ibagun sun tattara sun sauya sheka zuwa All Progressives Congress (APC).
Masu sauya sheƙar sun samu tarba mai kyau daga yar takarar mamban majalisar dokokin APC a mazabar Ilorin ta gabas, Hajiya Arinola Lawal, shugaban APC na gundumar, Rauf Adanla, da sauransu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Daga cikin waɗanda suka tarbi masu sauya shekar har da mai ba gwamna shawara ta musamman kan dabaru, Honorabul Saadu Salahu.
Meyasa Malaman suka yi wa gwamna Addu'a?
Malaman sun ce sun shirya taron Addu'o'in ne domin girmama Saadu Salahu kuma a cewarsu mai girma gwamna ya yi abin alherin da ya cancanci ƙara koma wa zango na biyu.
Mai magana da yawun masu shirya taron, Ustaz Abdullahi Olooto, ya ce sun saba gudanar da Addu'o'i domin nasarar gwamnatin AbdulRazaq tun lokacin da ya sa kafa a Ofis a 2019.
A cewarsa, a wannan lokacin sun yanke shawarin shirya gagarumin taron rokon Allah wanda ya haɗa manyan Malamai daga lungu da saƙom Ibagun.
Imam Hamzat Ayegbami ne jagoranci Addu'o'in tare da taimakon wasu malamai. A lakcar da ya gudanar, babban limamin Akuwo, Muhammad Ajibola, ya faɗi nagartar gwamnan Kwara.
Ya kuma yaba da gode wa mai girma gwamna AbdulRazaq bisa koƙarin tabbatar da zaman lafiya a jihar Kwara.
Jam'iyyar APC Ta Karbi Dubbannin Masu Sauya Sheka a Jihar Gombe
A wani labarin kuma Jigon siyasa da dubbannin mambobi aƙalla 5000 sun sauya sheka zuwa APC a jihar Gombe
Yayin da ake tunkarar zaben gwamnoni ranar 11 ga watan Maris, 2023, jam'iyyar APC mai mulki ta ƙara samun karfi.
Asali: Legit.ng