Kungiyoyin Magoya Bayan Tinubu Sun Jingine Sun Goyi Bayan Tazarcen Gwamnan PDP

Kungiyoyin Magoya Bayan Tinubu Sun Jingine Sun Goyi Bayan Tazarcen Gwamnan PDP

  • Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya samu babban goyon baya ana saura kwanaki 6 zaben gwamnoni
  • Gamayyar ƙungiyoyin magoya bayan Tinubu a kudu maso yamma sun tabbatar da goyon bayansu ga tazarcen Makinde
  • Kungiyoyin sun ziyarci mataimakin gwamnan a gidansa da ke Ibadan domin tabbatar da manufarsu

Oyo - Kwanaki 6 gabanin zaben gwamna a jihar Oyo, gamayyar ƙungiyoyin magoya bayan Asiwaju Bola Tinubu, sun ayyana cikakken goyon bayansu ga kudurin tazarcen gwamna Seyi Makinde.

Ƙungiyoyin sun ƙunshi Southern for Tinubu BAT Democracy; Yoruba Campaign for BAT da kuma Tinubu Campaign Movement, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Gwamna Seyi Makinde.
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde Hoto: Seyi Makinde
Asali: UGC

Sun bayyana matsayar da suka cimma ne yayin wata ziyara da suka kai gidan mataimakin gwamnan Oyo, Adebayo Lawal, da ke Ibadan, babban birnin jiha.

Sanarwan da suka fitar ranar Lahadi ɗauke da sa hannun Kodinetan gamayyar na ƙasa, Adebayo Moronsole, da jami'in hulda da jama'a, Emmanuel Adesanya, ta ce:

Kara karanta wannan

Kwana 7 Gabanin Zaben Gwamnoni, Hadimin Gwamnan APC Ya Yi Murabus, Ya Koma PDP

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ya kamata Makinde ya gyara zama a Ofishinsa domin ƙara inganta rayuwar mazauna Oyo, saboda haka gammayyar ƙungiyoyin magoya bayan Tinubu a kudu maso yamma na tare da shi da mataimakinsa."
"Yau mun zo gareka ne ranka ya daɗe ba don komai ba sai don mu ayyana cikakken goyon baya ga gwamna Makinde da mataimakinsa. Mun yi haka ne saboda kokarinsu a zangon farko."
"Muna da mambobi aƙalla 372,000 masu katin zaɓe, tuni masu haɗa kan jama'a suka fara shiga gida-gida tallata kudurin gwamna na neman tazarce. Mun ga ayyukan alheri da yawa a gwamnatin Makinde."

Da yake martani, mataimakin gwamnan ya yaba wa kungiyoyin bisa kokarinsu na aiki domin ci gaban kyawawan ayyuka a jihar Oyo, kamar yadda Guardian ta rahoto.

Lawal ya ce Makinde zai zama ɗaya daga cikin gwamnonin Oyo da ba za'a manta da su ba idan aka duba dumbin nasarorin da ya samu a zamanin mulkinsa.

Kara karanta wannan

Hukuncin da Kotun ƙoli ta Yanke Na Canjin Fasalin Kuɗi Zai Kasance Kyakkyawan Tushe Ga Mulkin Tinubu — Yahaya Bello

Ban da Alaka da Garabasar N20,000 Ga Duk Wanda Ya Zabi Abiodun, Gwamnan Ogun

A wani labarin kuma Gwamna Dapo Abiodun ya nesanta kansa da wata garabasa da ke yawo a soshiyal midiya da sunansa

A wata sanarwa ta hannun mai magana da yawun gwamnan, ya ce garabasar ƙarya ce kuma abokan karawar Abiodun ne ke kokarin ɓata masa suna.

Ya yi kira ga ɗaukacin mazauna jihar da su yi watsi da lamarin domin shiryayye ne domin shafa masa kashin kajin sayen kuri'u.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262