‘Yan Majalisa 10 da ba za su Koma Majalisa ba, Bayan Tsawon Shekaru Su na Wakilici
- Nan da kusan watanni 3 ake sa ran za a rantsar da sabuwar majalisar tarayya a Najeriya
- Za a samu sababbin Sanatoci da ‘Yan majalisar da suka doke wadanda suka dade a zauren
A wannan rahoto, mun tattaro jerin ‘yan majalisar wakilan tarayya da Sanatocin majalisar dattawan da suka ci taliyar karshe:
1. Kabiru Gaya (APC)
Tun shekarar 2007, Sanata Kabiru Gaya yake wakiltar Kudancin Kano a majalisar dattawa, wannan karo Abdurrahman Kawu Sumaila ya doke shi a jam’iyyar NNPP.
2. Ike Ekweramadu (PDP)
Sanata Ike Ekweremadu shi ne ‘dan majalisar da ya fi dadewa a kan mukami, ba zai koma ba a sakamakon shiga takarar Gwamnan Enugu da ya yi, amma bai dace ba.
3. James Manager (PDP)
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Sanata James Manager ba zai wakilci mutanen Delta a 2023, gawurtaccen ‘Dan siyasar ya hakura da kujerarsa, yana neman kujerar Gwamnan jiha a karkashin PDP.
4. Leo Ogor (PDP)
Shekaru 20 kenan Leo Ogor yana lashe zaben Majalisar wakilai a mazabar Isoko a Delta, shugaban marasa rinjayen ya rasa kujerarsa ga guguwar LP a wannan karo.
5. Yakubu Dogara
Shi ma Yakubu Dogara ba zai koma majalisa ba bayan tsawon shekaru yana wakiltar mutanen Bogoro/Dass/Tafawa Balewa, a zaben 2023 bai yi takara a PDP ba.
6. Ndudi Elumelu
A makon da ya gabata, Hon. Ngozie Okolie ta jam’iyyar LP ta doke Ndudi Elumelu na PDP wanda shi ne shugaban marasa rinjaye wanda ya fara zuwa majalisa tun 2007.
7. Yakubu Umaru Barde
A Yunin 2023 Yakubu Umaru ya zama ‘dan majalisa mai wakiltar Chikun/Kujuru, a wannan karo ‘dan takaran PDP ya doke shi da ratar kuri;u fiye da 10, 000.
8. Garbi Datti Muhammad
A zaben bana ne Garbi Datti Muhammad wanda aka fi sani da Babawo ya rasa kujerar Sabon Gari a jihar Kaduna ga tsohon abokin takararsa, Sadiq Ango Abdullahi.
9. Gideon Lucas Gwani
Gideon Gwani mai rike da kujerar masu tsawatar da marasa rinjaye a majalisar wakilai ya rasa kujerarsa bayan shafe shekaru kusan 16, ‘Dan takaran LP ya doke.
10. Nkeiruka Chidubem Onyejeocha
Shekaru kusan 16 Hon. Nkeiruka Chidubem Onyejeocha ta shafe shekaru 16 a majalisar tarayya, Amobi Godwin Ogah na jam’iyyar LP ya hana ta zarcewa a Abia.
Asali: Legit.ng