Zaben 2023: A Yayin Da PDP Da LP Suka Garzaya Kotu, SDP Ta Ce Ta Yarda Da Nasarar Tinubu

Zaben 2023: A Yayin Da PDP Da LP Suka Garzaya Kotu, SDP Ta Ce Ta Yarda Da Nasarar Tinubu

  • Jam'iyyar SDP ta tsame kanta daga cikin jam'iyyun da suka ce za su tafi kotu su kallubalanci sakamakon zaben shugaban kasa na 2023
  • Shugaban jam'iyyar na SDP na kasa, Shehu Gabam, ne ya sanar da hakan yayin taron manema labarai a Abuja, yana mai kira ga al'umma su zauna lafiya
  • Gabam, amma, ya ce duk wanda bai gamsu da zaben ba ya tafi kotu kuma ya kyautata zaton cewa kotunan Najeriya za su yi wa dukkan bangarorin adalci

FCT Abuja - Jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) ta ce ba za ta kallubalanci sakamakon zaben shugaban kasa da hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta sanar ba.

Shehu Gabam, shugaban SDP na kasa, ya yi jawabi wurin taron manema labarai a Abuja, The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Sakamakon Zaben 2023: Atiku Ya Bayyana Matakin Karshe Da Zai Dauka Idan Bai Yi Nasara A Kotu Ba

Collation Centre
Cibiyar tattaro sakamakon zaben Najeriya da ke Abuja. Hoto: The Cable.
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce duk da cewa an samu matsala na kayan aiki, SDP ba za ta kallubalanci ayyana Bola Tinubu na jam'iyyar APC a matsayin zababben shugaban kasa ba.

Shugaban na SDP ya ce:

"Duk da kallubale da aka gani kararra tattare da zaben da damuwa da masu ruwa da tsaki suka nuna, SDP ta goyi bayan zabi da karshe da aka yi kuma yadda yan Najeriya da dama daga bangarori daban-daban suka nuna, kuma mun amince da sakamakon zaben.
"Mun yaba wa INEC karkashin jagorancin Farfesa Yakubu saboda aikin da ya yi duk da kallubalen da ke gabansa.
"An yi zabe kuma an samu wanda ya yi nasara, abin da ya dace don cigaban kasar mu shine duk masu korafi su bi hanyar da ta dace.
"Jam'iyyar mu ta yi imani cewa bangaren shari'a za ta iya magance abubuwan da za su taso dangane da zaben da damuwan mutane."

Kara karanta wannan

Karin Bayani: "Ba Zan Yarda Ba" Peter Obi Ya Maida Martani Mai Dumi Kan Nasarar Tinubu

Gabam ya kuma yi kira ga bangaren shari'ar ta yi wa duk wani wanda ya yanke shawarar kallubalantar sakamakon zaben adalci.

Ya ce:

"Dole dokar mu ta yi aiki ko da wanenen ya kai kara."

Peter Obi na jam'iyyar Labour, LP, da Atiku Abubakar na PDP sun ce za su tafi kotu don kallubalantar sakamakon zaben.

Atiku: Zan bar wa Allah idan ban yi nasara a kotu ba

Dan takarar shuganan kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar da jam'iyyars sun ki amincewa da sakamakon zaben shugaban kasa na 2023.

Hakan yasa suka ce za su tafi kotu don kallubalantar nasarar Bola Tinubu.

Amma, Atikun ya ce idan kotu ba ta share masa hawayensa ba zai hakura ya bar wa Allah lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164