Kuri'un Da Peter Obi Yaja Mana Asara Sun Yi Kaɗan Su Sanya Ya Zama Shugaban Ƙasa, Atiku
- Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, yace suna maraba da Peter Obi a koda yaushe
- Atiku ya bayyana asarar da Peter Obi ya janyowa jam'iyyar PDP a zaɓen shugaban ƙasa da ya gabata
- Ɗan takarar yace ƙofa a buɗe take su yi ƙawance da Peter Obi na jam'iyyar Labour Party idan har yana son hakan
Abuja- Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) Atiku Abubakar, yace jam'iyyar a shirye take ta ƙulla ƙawance da jam'yyar Labour Party (LP)
Atiku Abubakar ya bayyana hakan ne a birnin tarayya Abuja, yayin wani taro da manema labarai a ranar Alhamis. Rahoton The Cable.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana cewa PDP tayi asarar ƙuri'u sosai a hannun Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na Labour Party, a zaɓen ranar Asabar.
“Eh gaskiya ne ya kwashe mana ƙuri'u a yankin Kudu maso Yamma da Kudu maso Kudu, amma lallai hakan yayi kaɗan ya sanya ya zama shugaban ƙasa." A cewar sa
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kun san cewa kana buƙatar samun ƙuri'u daga ko ina kafin ka zama shugaban ƙasa. Saboda haka ni a wajena, mu na maraba da tattaunawa da Peter Obi, a shirye muke mu tattauna da shi."
“Bana tunanin zamu samu wata matsala idan yana son ya tattauna da PDP. Ko mu yi haɗaka ko akasin hakan."
Atiku Abubakar ya bayyana cewa Peter Obi ya bar jam'iyyar ne inda ya koma Labour Party, bayan gwamnonin PDP sun haƙiƙance cewa dole a cikin su ne za a samu ɗan takarar shugaban ƙasa da mataimakin sa. Rahoton Vanguard
Atiku yace shi a maimakon ya bar PDP, sai ya tsaya suka ja daga da gwamnonin inda daga ƙarshe ya samu nasarar lashe tikitin takarar shugaban ƙasa na jamiyyar PDP.
2023: Ban da Masaniyar Tinubu Na Yunkurin Neman Sulhu, Atiku Abubakar
A wani labarin na daban kuma, Atiku Abubakar yace baya da masaniya kan cewa zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu, yana. neman sulhu da shi.
Jam'iyyar APC dai ta ƙafa wani kwamiti wanda zai tattauna da ƴan takarar da suka sha kaye a zaɓen shugaban ƙasa domin samun sulhu.
Asali: Legit.ng