2023: Ban da Masaniyar Tinubu Na Yunkurin Neman Sulhu, Atiku Abubakar
- Atiku Abubakar ya ce babu wani gwamna da ya zo neman zama da shi a gidansa tun bayan kammala zaɓe
- Tsohon mataimakin shugaban kasan ya ce bai san komai game da yunkurin neman sulhun Tinubu ba
- Gwamnan Ondo ya yi ikirarin cewa Tinubu ya kafa kwamitocin da zasu gana da yan takarar da suka sha kasa
Abuja - Ɗan takarar da ya nemi zama shugaban kasa a inuwar PDP a zaben ranar Asabar, Atiku Abubakar, yace bai san da shirin Bola Tinubu na neman sulhu da su ba.
Punch ta tattaro cewa APC ta kafa kwamitocin sulhu da zasu zauna da Atiku, Peter Obi na Labour Party da sauran yan takarar da suka fafata a zaben da ya gabata.
A cewar gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu, kwamitin da aka kafa zai maida hankali wajen warware damuwar yan takarar kana ya jawo su yi aiki da zababben shugaban kasa don ci gaban Najeriya.
Bayan Amurka Da Birtaniya, Sarkin Wata Babban Kasa Ya Sake Taya Tinubu Murnar Cin Zaben Shugaban Kasa
Gwamna Akeredolu ya bayyana haka ne a wata sanarwa da sakatarensa na watsa labarai, Richard Olatunde, ya fitar ranar Laraba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Zababben shugaban kasa ya kafa kwamitocin da su zauna da mutanen da suka fafata a zaɓe domin mu ci gaba da kokarin share hawayen kasa. Ina cikin ɗaya daga kwamitocin."
"Zamu neme su mu zauna mu roki alfarmar su zo a yi aiki kafaɗa da kafaɗa," inji gwamnan Ondo a cikin sanarwan.
Atiku ya maida martani
Amma yayin da aka tambaye shi kan batun a wurin taron manema labarai a Abuja ranar Alhamis, domin tabbatar da ko gwamnonin sun zo, Atiku ya ce bai da labari ko kaɗan.
"Maganar gaskiya ban san komai a kai ba, ina gida tsawon kowace rana amma ban samu labarin wani gwamna ya zo gani na ba," inji tsohon mataimakin shugaban kasan, rahoton Daily Trust ya tabbatar.
Babu Sauran Gardama Tinubu Ne Zabin Ƴan Najeriya, Adamu
A wani labarin kuma Sanata Abdullahi Adamu ya ce zaben bana ya tabbatar da waye yan Najeriya suke kauna
A cewar shugaban jam'iyya mai mulki na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, babu sauran tababa, ɗan takarar APC ne zabin yan Najeriya.
Adamu ya kuam soki matakin PDP na LP na kira ga INEC fa sake baki ɗaya zaben da ya gudana ranar Asabar.
Asali: Legit.ng