2023: Babu Sauran Gardama Tinubu Ne Zabin Ƴan Najeriya, Adamu
- Sanata Abdullahi Adamu ya nuna farin ciki da samun nasarar Bola Ahmed Tinubu a zaben da ya gudana ranar Asabar
- Shugaban APC na ƙasa ya ce nasarar Tinubu ta ƙara fayyace cewa shi ne zabin da yan Najeriya ke fata
- Ya yi Allah wadai da jam'iyyar PDP da Labour Party, waɗanda suka nemi INEC ta soke zaben ranar Asabar
Abuja - Shugaban APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya ce ta tabbata ɗan takararsu na shugaban kasa a zaben da aka kammala, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ne zaɓin al'umma.
Channels tv ta tattaro cewa yayin da yake jawabi a wurin taron yan jarida, Adamu ya ce jam'iyyar APC ta fito ta nuna farin ciki da murnar wannan nasara tare da 'yan Najeriya.
Ya ce sun haɗa wannan taron manema labarai ba don komai ba sai don miƙa godiya da yabo ga yan Najeriya bisa wannan nasara da suka samu a zaɓen 25 ga watan Fabrairu, 2023.
Ya kara jaddada cewa yan Najeriya sun aminta da nagartar Bola Tinubu shiyasa suka damƙa masa amana domin ya share masu hawayen da suke fama da shi a ƙasar nan.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A madadin jam'iyyar APC, Sanata Abdullahi Adamu ya yi fatan Alheri tare da miƙa hannun abota ga dukkan 'yan takarar da suka nemi zama shugaban kasa amma ba su samu nasara ba.
Haka nan shugaban APC ya yi Allah wadai da abinda PDP da Labour Party suka aikata, jam'iyyun da suka bukaci hukumar zabe mai zaman kanta ta soke zaben shugaban kasa.
Adamu ya yi kira ga yan Najeriya sun tashi tsaye kan masu neman a soke zaɓe kana ya shawarci duk wanda bai gamsu da sakamakon ba ya kai ƙara Kotu.
A cewarsa kiraye-kirayen a canza zaɓe wani yunkuri ne na jefa kasar nan cikin bala'i, kamar yadda The Cable ta ruwiato.
Ni Na Lashe Zaben Shugaban Kasa Kuma Zan Tabbatar da Haka, Obi
A wani labarin kuma Ɗan takarar Labour Party, Peter Obi, yace ba zai yarda da sakamakon zaben da INEC ta sanar ba
Mista Obi, wanda ya zo na uku a yawan kuri'u, ya yi ikirarin cewa shi da abokin takararsa ne suka lashe zabe amma aka kwace masu.
Ya ce zai nufi Kotu domin kwato hakkinsa da aka masa karfa-karfa kuma hakan ba sabon abu bane a tarihin rayuwarsa.
Asali: Legit.ng