2023: Gwamna Wike Ne Ƙashin Bayan Nasarar Tinubu a Ribas, APC
- Jigon jam'iyyar APC kuma mamban kwamitin kamfen shugaban kasa ya faɗi irin taimakon da Wike ya yi wa Tinubu
- Tony Okocha, ya ce gwamanan na PDD ne kashin bayan nasarar APC a jihar Ribas domin ya taimaka fiye da tunani
- A karo na farko tun shekarar 2015, jam'iyyar APC ta samu nasara a zaben gudaban kasan da aka gudanar a Ribas
Rivers - Kwamitin kamfen shugaban kasa na jam'iyyar APC (PCC) ya ce gwamna Nyesom Wike ne ƙashin bayan nasarar da Bola Ahmed Tinubu ya samu a jihar Ribas.
PCC-APC na jihar Ribas ya bayyana cewa ba don jajircewar gwamna Wike ba,Tinubu ba zai samu ko kaso 25% da doka da tanada ba a jihar, kamar yadda Vanguard ta rahoto.
Da yake karin haske ranar Alhamis, mamban kwamitin PCC kuma jagoran tawagar kamfen APC mai zaman kanta a Ribas, Tony Okocha, ya yaba wa Wike.
A cewarsa, ya zama wajibi a jinjinawa gwamnan bisa dumbin goyon bayan da ya ba APC har ta samu nasara a jihar karon farko tun shekarar 2015.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mista Okocha ya ce:
"A tsaya faɗin cewa Wike ya taka rawar gani wurin nasarar ɗan takarar mu na shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ba'a masa adalci ne, gwamnan shi ne kayan aiki, shi ne ƙashin bayan nasarar mu."
"Da kansa ya gaya wa mutanen jihar Ribas su zaɓi wanda zai kaunaci jiharsu, ya taimaka mata. Ya jawo mutane ya tattara bil Adama da dukiyarsa domin tabbatar da mun samu nasara, dole mu jinjina masa."
"Kuɗin da muke da u ba zasu usa tunkarar zaɓe ba, amma ina muka samu kuri, ta ya muka samu nasara, wa ya taimaka muka samu kaso sama da 40 na kuri'un Ribas? Muna yaba wa Wike kuma mun gode."
Daga nan ya yi kira ga zababben shugaban ƙasa da mataimakinsa su ɗauki wannan nasara a matsayin nauyi daga Allah kuma su ja kowa a jiki, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Jigon PDP ya yi watsi da gwamna Okowa
A wani labarin kuma Bayan Tinubu Ya Ci Zaɓe, Babban Jigon PDP Ya Jingine Tafiyar Atiku, Ya Koma Jam'iyyar APC
Yayin da masoya da masu fatan alheri ke ci gaba da murna da nasarar Bola Tinubu, jam'iyyar PDP ta rasa ɗaya daga cikin jiga-jiganta a jihar Delta.
Asali: Legit.ng