Atiku da Peter Obi Sun Ki Sallamawa Bola Tinubu, Sun Fadi Matsayar da Za Su Dauka

Atiku da Peter Obi Sun Ki Sallamawa Bola Tinubu, Sun Fadi Matsayar da Za Su Dauka

  • Atiku Abubakar da ya yi takarar shugabancin kasa a jam’iyyar PDP bai yarda da zaben 2023
  • Shi ma Peter Obi na LP ya kalubalanci sakamakon zaben da aka fitar, ya nuna za su shiga kotu
  • Jam’iyyar NNPP da ta ba Rabiu Kwankwaso takara ta na ganin INEC ba tayi zaben kwarai ba

Abuja - ‘Dan takaran PDP a zaben shugaban kasa, Atiku Abubakar da Peter Obi na jam’iyyar LP sun ce za su shigar da kara a kotu a kan zaben 2023.

‘Yan takaran sun bayyana haka ne bayan da aka ayyana Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zabe. Daily Trust ta fitar da rahoton a ranar Alhamis.

Dino Melaye wanda shi ne Daretan hulda da jama’a na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa a PDP ya fitar da wani jawabi a yammacin Laraba.

Kara karanta wannan

Nasarar Obi a Legas da Abubuwan ban Mamaki 10 da suka Girgiza Al’umma a Zabe

Sanata Dino Melaye ya ce babu ja da baya a yunkurinsu na ganin sun karbe nasarar da suka samu a zabe, jigon na PDP yana ganin an yi magudin zabe.

Ba za ta sabu ba - Dino

"Kira ga daukacin magoya bayan Atiku Abubakar a duk fadin Duniya da cewa ka da ku damu. Ko da an yi kuka yanzu, murna ta na tafe daga baya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mummunar rashin adalcin nan ba zai tafi a haka ba. Babu ja da baya a wajen gwagwarmayarmu na karbo nasararmu da aka sace. Za mu samu nasara."

- Dino Melaye

Bola Tinubu
INEC ta ba Bola Tinubu satifiket Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

A rahoton dai, an ji Sanata Yusuf Datti Baba-Ahmed wanda ya shiga takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar LP yana cewa za su nemi hakkinsu a kotu.

Yusuf Datti Baba-Ahmed ya yi magana

Yusuf Datti Baba-Ahmed ya ce za su kalubalanci nasarar APC a zaben ne ta hanyar lalama.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: El-Rufai ya taya Tinubu murnar lashe zabe, ya fadi abin da Tinubu zai yiwa kasa

Da ya kira wani taron ‘yan jarida a madadin Peter Obi a ranar Laraba, tsohon Sanatan ya tabbatarwa magoya bayansu cewa ba su yarda da zaben nan ba.

A cewar Datti Baba-Ahmed zaben da aka yi bai cika sharudan gaskiya da adalci ba, amma duk da haka ya godewa dinbin mutanen da suka zabi jam’iyyarsu.

Farfesa Rufai Alkali a matsayinsa na shugaban NNPP na kasa ya soki hukumar INEC, yake cewa zaben bai yi kyau ba, ya bukaci a shirya wani sabon zabe.

Abubuwan ban mamaki 11

A jerin abubuwan ban al'ajabi a zaben 2023, mun kawo batun Peter Obi da ya samu kuri’u 582,454 a Legas, ya jijjiga Bola Tinubu da ya samu kuri'u 572, 606.

Sannan ‘Dan takaran PDP, Atiku Abubakar ya rasa jihar Delta duk da ya dauko Gwamna Ifeanyi Okowa, NNPP kuwa ta takawa kowa burki a jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng