Rundunar Yan Sanda Ta Haramta Bukukuwan Da Zanga-Zanga Kan Zaben Shugaban Kasa a Kaduna

Rundunar Yan Sanda Ta Haramta Bukukuwan Da Zanga-Zanga Kan Zaben Shugaban Kasa a Kaduna

  • Rundunar yan sandan jihar Kaduna ta dauki mataki domin hana barkewar rikici da karya doka da oda a jihar
  • Yan sanda a jihar Kaduna sun hana yin bukukuwa ko zanga-zanga a kan zaben shugaban kasa da na yan majalisar tarayya da aka kammala a jihar
  • Kakakin yan sandan jihar ya ce duk wanda aka kama da keta wannan doka zai fuskanci hukunci a hannun doka

Kaduna - Rundunar yan sandan jihar Kaduna ta sanar da haramta wa magoya bayan jam'iyyun siyasa yin bukukuwa ko zanga-zanga kan zaben shugaban kasa da na majalisar tarayya da aka kammala.

A cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Laraba, 1 ga watan Maris, kakakin yan sandan jihar, Mohammed Jalige, ya ce duk wanda aka kama ya keta dokar zai fuskanci hukunci, jaridar The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Zaben Shugaban Kasa Na 2023: Sheikh Bala Lau Ya Gargadi Yan Siyasa Kan Furta Maganganu Da Ka Iya Tada Rikici

Jami'an yan sanda rike da bindigogi
Rundunar Yan Sanda Ta Haramta Bukukuwan Da Zanga-Zanga Kan Zaben Shugaban Kasa a Kaduna Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Jalige ya ce:

"Rundunar na fatan sanar da jama'a cewa an haramta duk wasu nau'i na bukukuwa da gangami daga magoya bayan jam'iyyun siyasa kan wadanda suka yi nasara ko suka fadi a zaben shugaban kasa da na majalisar tarayya da aka kamma a a jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ba za a lamunci duk wani aikin ganganci na karya dokar haramcin ko take doka da oda ba, duk wanda ya aikata hakan zai dandana kudarsa a hannun yan doka."

An zuba jami'an tsaro domin tabbatar da dokar

Ya kara da cewar an tura hukumomin tsaro jihar sannan an umurcesu da su tabbatar da ganin cewa dokar ta yi aiki, rahoton Punch.

Ya ce:

"Ana gargadin duk mutanen da ke da niyar keta dokar da su guji aikata hakan, domin rundunar tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro sun shirya yin maganin irin wadannan mutane daidai da doka.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Haramta Zanga-Zanga

"Rundunar na amfani da wannan damar wajen kira ga al'umma da kada su yi kasa a gwiwa wajen marawa hukumomin tsaro baya wajen aiwatar da ayyukansu na kare rayuka da dukiyoyin jama'ar jihar Kaduna."

Tinubu na shirin sauya farkon sunan gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu

A wani labari na daban, zababben shugaban kasa, Bola Tinubu, ya bayyana shirinsa na son sauyawa gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu farkon sunansa.

Da yake jawabi, Tinubu ya bayyana cewa lallai Gwamna Atiku Bagudu ya yi aiki tukuru wajen tabbatar da ganin cewa jam'iyyar APC mai mulki ta yi nasara a babban zaben shugaban kasar.

Bagudu dai na dauke da suna irin na babban abokin adawar Tinubu kuma dan takarar PDP, Atiku Abubakar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng