Tinubu Ya Yi Wa Yan Najeriya Babban Alkawari A Jawabinsa Bayan Lashe Zabe

Tinubu Ya Yi Wa Yan Najeriya Babban Alkawari A Jawabinsa Bayan Lashe Zabe

  • Zabbabben shugaban Najeriya Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya sha alwashin bautawa Najeriya da duk karfinsa
  • Tinubu ya dauki alkawarin yayin da ya ke jawabin godiya bayan da hukumar INEC ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa na ranar Asabar
  • Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta sanar da Asiwaju Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben da sama da kuri'a miliyan 8

FCT, Abuja - Zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, a ranar Laraba, ya tabbatarwa da yan Najeriya cewa zai zama bawansu zai kuma bautawa Najeriya da duk karfinsa.

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da ya ke kira ga jam'iyyun adawa da masu sukar sa da su hada hannu da shi don ciyar da kasar gaba.

Bola Tinubu
Tinubu ya yi alkawarin bautawa yan Najeriya. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

"Ba A Taba Yin Ingantaccen Zabe Na Gaskiya Kamar Na 2023 Ba A Najeriya", Kashim Shettima

A jawabin da ya yi na lashe lashe a birnin tarayya Abuja, Tinubu ya ce

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Mu hada kai muyi aiki tare. Nayi alkawari zan yi aiki da ku,''
"A karshe ina godiya ga yan Najeriya saboda imanin da suka yi da dimokradiyya. Zan zama shugaba mai adalci ga dukkan yan Najeriya. Zan rika bibiyan burinku, in karfafa muku gwiwa da tallafawa hazakarku don sama'r da al'umma da za mu yi alfahari da ita."

Tinubu ya kuma yi kira ga sauran abokan karawarsa da su taho su hada kai suyi aiki tare don gina kasa.

Wasu cikin wadanda suka halarci taron

A wajen yana tare mataimakinsa, Sanata Kashim Shettima, shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu, da gwamnonin APC, da wasu da dama.

Da ya ke karin bayani, tsohon gwamnan na Lagos, ya yabawa yan Najeriya, musamman wanda suka zabi jam'iyyun adawa, yana mai cewa hakan ya taimaka wajen tabbatar da dimukradiyya a Najeriya.

Kara karanta wannan

“Mu Muka Ci Zaben Shugaban Kasa, Za Mu Kwato Hakkinmu” – Inji Datti Baba-Ahmed

Punch ta ruwaito cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana Tinubu tun da safiyar Laraba, dan takarar APC a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa na ranar Asabar, a matsayin zababben shugaban kasa.

An bayyana Tinubu a matsayin zababben shugaban kasa bayan da mai shekaru 70 din ya samu kuri'a 8,794,726 don lashe zaben shugaban kasa na 2023.

Shugaban hukumar INEC, Prof. Mahmood Yakubu, ya sanar da Tinubu a matsayin wanda ya yi nasara a cibiyar tattara sakamakon zabe da ke Abuja.

Tinubu ya lashe zaben inda ya kada sauran yan takarar - dan takarar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar;dan jam'iyyar LP, Peter Obi; da kuma dan takarar jam'iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso.

A bangare guda kun ji cewa Tinubun ya lashe zabuka a jihohi 12 na kasar ne don samun zama shugaban kasa.

Daga cikin jihohin akwai jihar Ekiti, Zamfara, Kogi.

Kara karanta wannan

Na Hannun Dama Ya Ba Tinubu Shawara Ya Jawo Kwankwaso da Peter Obi a Gwamnati

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164