Jerin Gwamnonin Da Suka Lashe Kujerun Sanatoci a Jihar Su
- Gwamnoni da dama sun nemi takarar kujerar sanatoci a jihohin su domin zuwa majalisar dattawan Najeriya
- Sai dai wasu daga cikin gwamnonin jikin su ya gaya musu domin ba suyi nasara ba a takarar da suka yi
- Ƴan kaɗan ne kawai daga cikin gwamnonin da suka yi takarar kujerun sanatoci suka samu nasara a zaɓen
Wani lamari mai matuƙar ban mamaki shine yadda wasu gwamnonin da suka so su wakilci mutanen su a majalisar dattawa, suka sha kashi a hannun ƴan takarar jam'iyyun adawa.
Wannan zaɓen da aka kammala na shugaban ƙasaa da na ƴan majalisun tarayya a ranar Asabar, ya nuna gazawar wasu gwamnoni a yankunan su, da kuma yadda mutane suka tsaya suka kare abinda suke ra'ayi.
Yayin da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ke cigaba da tattara sakamakon zaɓen shugaban ƙasa, ƴan takarar da suka neman kujerun sanatoci tuni suka san matsayar su.
Sakamakon Zabe: Tsoffin Gwamnoni da Ministoci, Sanatoci da Wasu Manya Sun Huro Wa INEC Wuta Kan Abu 1
Gwamnoni biyu sun yi nasara
Sai dai daga cikin gwamnonin da suka yi takarar sanata a jihohin su, guda biyu ne kawai suka samu nasara.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ga jerin su:
Gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi
Gwamna David Umahi ya samu nasarar lashe zaɓen sa domin wakiltar Ebonyi ta Kudu a majalisar dattawa.
Umahi, wanda shine ɗan takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC), ya samu ƙuri'u 28,378, inda ya doke ɗan takarar Labour Party, Linus Okorie, wanda ya samu ƙuri'u 25,496
Gwamna Abubakar Bello na jihar Neja
A ranar Litinin, 27 ga watan Fabrairun 2023, gwamna Abubakar Bello na jihar Neja ya lashe zaɓen sanatan Neja ta Arewa a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar All Progressives Congress (APC).
Gwamna Bello, ya samun nasara bayan ya samu ƙuri'u masu rinjaye a zaɓen inda ya samu ƙuri'u 100,197, domin kayar da ɗan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Shehu Muhammad Abdullahi, wanda ya samu ƙuri'u 88,153.
Gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu, yakamata ace ya shigo cikin wannan jerin, sai dai a zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, hukumar INEC ta bayyana zaɓen jihar a matsayin ba kammalalle ba saboda zargin an yi ba daidai ba a cikin sa.
Duniya Rawar Ƴan Mata: Lalong Ya Tunkuyi Ƙasa a Takarar da Yayi Ta Sanata
A wani labarin na daban kuma, gwamnan jihar Plateau yasha kashi a takarar nemsn kujerar sanata.
Gwamnan ya sha kashi ne a hannun ɗan takarar jam'iyyar PDP.
Asali: Legit.ng