Hukumar INEC Ta Ƙara Ɗage Tattara Sakamakon Zaɓen Shugaban Ƙasa

Hukumar INEC Ta Ƙara Ɗage Tattara Sakamakon Zaɓen Shugaban Ƙasa

  • Hukumar zaɓe ta INEC ta sanar da ɗage cigaba da tattara sakamakon zaɓen shugaban ƙasa
  • Hukumar ta INEC ta sanar da cewa tana jiran isowar sakamakon wasu jihohi kafin ta cigaba da tattara sakamakon
  • Ya zuwa yanzu dai hukumar ta bayyana sakamakon zaɓe a jihohi da dama, inda manyan jam'iyyun dake takara kowacce ta samu nata rabon

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta sanar da ɗage tattara sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na zuwa wasu ƴan sa'o'i. Rahoton Daily Trust

Hukumar zaɓen ta INEC ta sanar da cewa zata cigaba da tattara sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da misalin ƙarfe uku da rabi (3:30pm) na ranar yau Talata. Rahoton Channels Tv

Sai dai, har ya zuwa lokacin da hukumar tace zata cigaba da tattara sakamakon zaɓe, bata cigaba ba, domin har yanzu ba a cigaba da bayyana sakamakon zaɓen na shugaban ƙasa ba.

Kara karanta wannan

Da Zafi Zafi: Jam'iyyun PDP, LP, ADC Sun Buƙaci Shugaban INEC yayi Murabus Tare Da Sake Sabon Zaɓe

A ranar Lahadi ne dai hukumar INEC ta fara tattara sakamakon zaɓen na shugaban ƙasa a babban ɗakin taro na ƙasa da ƙasa a birnin tarayya Abuja.

Tattara sakamakon zaɓen shugaban ƙasar na ranar Litinin, an kammala shi ne wasu ƴan mintoci kaɗan bayan ƙarfe goma na dare.

Shugaban hukumar zaɓen ta ƙasar Farfesa Mahmood Yakubu, ya ɗage tattara sakamakon zaɓen zuwa ƙarfe sha ɗaya na safen ranar Talata, domin bayar da dama ga jami'an tattara sakamakon zaɓen na jihohi su kammala tattara na su sakamakon.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Amma da yake magana da ƴan jarida ranar Talata, kwamishinan hukumar zaɓen na ƙasa, Festus Okoye, yayi bayanin cewa hukumar ta ɗage lokacun da ta sanya na cigaba da tattara sakamakon zaɓen, har na zuwa wasu ƴan sa'o'i kaɗan.

Ya bayyana cewa a yanzu haka, akwai sakamakon zaɓen na jihohi biyar a hannu, amma hukumar na jiran aƙalla sauran wasu jihohi goma su kawo sakamakon zaɓen su a yau.

Kara karanta wannan

Zaɓen 2023: Ƴan Daba Sun Tarwatsa Jami'an INEC Sun Hana a Bayyana Sakamakon Zaɓe

Ya zuwa yanzu dai an bayyana sakamakon zaɓen jihohi kusa goma sha uku, inda manyan jam'iyyun kowacce ta samu rabon ta.

Peter Obi Ya Lallasa PDP a Jihar Abokin Takarar Atiku Abubakar

A wani labarin na daban kuma, Peter Obi ya lallasa Atiku Abubakar a jihar abokin takarar sa, Ifeanyi Okowa.

Ɗan takarar na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi, ya samu ƙuri'u masu rinjaye sosai a jihat Delta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng