INEC Ta Ayyana Zaben Zamfara Ta Tsakiya a Matsayin Ba Kamalalle Ba
- Hukumar zabe ta INEC ta ayyana zaben sanata mai wakiltan Zamfara ta tsakiya a matsayin ba kamalalle ba
- Baturen zabe na mazabar Gusau/Tsafe ya ayyana zaben dan majalisar wakilai na mazabar a matsayin ba kamalalle ba
- Jami'an hukumar zabe sun bayyana INEC za ta sanar da sabon rana da za a sake zaben cike gurbi
Zamfara - Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta a ranar Talata, 28 ga watan Fabrairu, ta ayyana zaben sanata mai wakiltan Zamfara ta tsakiya a matsayin ba kamalalle ba, jaridar Punch ta rahoto.
Baturen zaben yankin, Farfesa Ahmad Galadima, ya bayyana cewa zaben da aka soke ya shafi rumfunan zabe akalla 74 daga yankuna 19 da aka yi rijista na Bungude, Gusau da Tsafe
A cewarsa, jimlar katunan zabe da aka karba a yankin sun kasance 43,881, wanda ya fi yawan tazarar da ke tsakanin jam'iyyu biyu da suka fi yawan kuri'u.
Dan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya samu kuri'u 93,120 yayin da dan takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) yake da kuri'u 79,444.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Galadima ya ce:
"Da tazarar 13,676, abun da za a iya yi kawai shine ayyana zaben a matsayin ba kamalalle ba."
An soke zaben rumfuna 38 a Gusau da Tsafe
Hakazalika, baturen zaben INEC a mazabar tarayya ta Gusau/Tsafe, Dr. Aminu Dabai shima ya bayyana soke rumfunan zabe 38 daga kananan hukumomin Gusau da Tsafe.
A cewar Dabai, sakamakon zabe daga yankuna bakwai bai da tazara mai yawa tsakanmin PDP da APC.
Sakamakon haka, ya ayyana zaben mazabar tarayya ta Gusa/Tsafe a matsayin ba kamalalle ba.
Jami'an na INEC sun bayyana cewa hukumar zaben za ta sanar da sabon rana da za a yi zaben cike gurbi.
A soke zaben shugaban kasa, Olusegun Obasanjo
A wani labari na daban, tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo ya bukaci hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta da ta soke zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu.
Obasanjo ya bukaci hakan ne domin a cewarsa ta haka ne kawai za a iya kubutar da kasar daga hatsari da annobar da ke jiranta kan zargin magudi a zaben.
Asali: Legit.ng