INEC Ta Ayyana Shekarau da Ya Koma PDP a Matsayin Wanda Ya Ci Zaben Sanata a NNPP

INEC Ta Ayyana Shekarau da Ya Koma PDP a Matsayin Wanda Ya Ci Zaben Sanata a NNPP

  • Ibrahim Shekarau ne zai dare kujerar Sanatan Kano ta tsakiya ba Sanata Rufa’i Sani Hanga ba
  • NNPP ta maye gurbinsa da Rufa’i Sani Hanga a dalilin barin Jamiyyar NNPP da ya yi zuwa APC
  • A wurin INEC, har gobe tsohon Gwamnan Kano da ya sauya-sheka zuwa PDP shi ne ‘dan takara

NNPP - Malam Ibrahim Shekarau shi ne wanda aka sanar a matsayin wanda ya lashe zaben Sanata na mazabar Kano ta tsakiya a majalisar dattawa.

Daily Trust ta rahoto cewa hukumar INEC ta bakin malamin zaben shiyyar jihar Kano ta tsakiya, Farfesa Tijjani Hassan Darma ta ce NNPP ta ci zabe.

Farfesa Tijjani Hassan Darma ya ayyana sunan Ibrahim Shekarau a matsayin ‘dan takaran da ya yi galaba a kan sauran jam’iyyu da kuri’u 456,787.

Wanda ya zo na biyu a zaben shi ne Abdulkarim Abdussalam Zaura na APC mai kuri’u 168, 677.

Kara karanta wannan

Zuwa Yanzu APC Ta Samu Sanatoci 38, PDP Ta Lashe 21, NNPP Ta Ci Kujeru a Majalisa

Ibrahim Shekarau wanda yanzu ‘dan PDP ne sun sha kashi a zaben, ‘yar takarar jam’iyyar PDP watau Laila Buhari ta zo ta uku ne a zaben na bana.

NNPP.
Kamfen NNPP a Dala @KYusufAbba
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Matsayar da hukumar zabe na kasa ta bada ya jefa al’ummar Kano cikin wani irin hali ganin cewa su na hango Sanata Rufa’i Sani Hanga a majalisa.

Sanata mai-ci Ibrahim Shekarau ya na cikin wadanda suka shiga jam’iyyar NNPP da farko, amma sai daga baya ya sauya-sheka zuwa jam’iyyar PDP.

Sauya-shekar da tsohon Gwamnan ya yi ya jawo ya salwantar da takarar Sanata da aka ba shi, kuma ya sanar da INEC cewa ya fasa shiga zabe.

Duk da wasikar da tsohon Ministan ilmin ya rubuta, hukumar zabe ba ta canza sunansa a matsayin ‘dan takara ba, wannan ya jawo NNPP ta shiga kotu.

Kara karanta wannan

El-Rufai Ya Gagara Kawowa Tinubu Jihar Kaduna, Atiku da PDP Sun Ragargaji APC

Ibrahim Adam wanda yana cikin kwamitin yakin neman zaben NNPP, ya ce kotun tarayya da na daukaka kara sun umarci INEC ta canza sunan ‘dan takaran.

Da yake bayani a Facebook, Adam ya ce kararsu ta na kotun koli kuma abin da suke sa rai shi ne hukumar zabe tayi biyayya ga umarnin da Alkalai suka yi.

Zaben 'Yan Majalisa a 2023

A wani rahoto da aka fitar, kun ji labari Jam'iyyar APC ta sha gaban PDP, LP da NNPP a tseren zuwa Majalisar Dattawa a zaben shekarar shekarar nan.

Watakila abin da ya fi ba jama’a mamaki shi ne kujerun Sanatoci da Jam’iyyar SDP ta samu a yankin Arewa ko kuma nasarar Ahmad Lawan a Yobe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng