Sakamakon Zamfara: Bola Tinubu Ya Lallasa Atiku a Zaben Shugaban Kasa

Sakamakon Zamfara: Bola Tinubu Ya Lallasa Atiku a Zaben Shugaban Kasa

  • Dan takarar shugaban kasa na APC mai mulki ya lashe mafi yawan kuri'un da Zamfarawa suka kaɗa ranar Asabar
  • Bola Tinubu ya lallasa Atiku da Rabiu Musa Kwankwaso a kananan hukumomi 10 cikin 14 da ke jihar
  • Ana ci gaba da tattara sakamakon zaben da ya gudana ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023

Zamfara - Ɗan takarar shugaban ƙasa karƙashin inuwar jam'iyyar APC mai mulki, Bola Tinubu, ya lallasa babban abokin hamayyarsa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, a jihar Zamfara.

Nasarar Tinubu ta tabbata ne bayan ayyana sakamakon zaben shugaban kasa da ya gudana a faɗin kananan hukumomi 14 na jihar Zamfara kuma hukumar zaɓe INEC ta sanar.

Bola Ahmed Tinubu.
Tinubu ya lashe zabe a Zamfara Hoto: ABAT
Asali: Facebook

Rahoton Premium Times ya bayyana cewa Tinubu ya samu galaba a kananam hukumomi 12, yayin da Atiku ya lashe ragowar guda biyu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Peter Obi Ya Lallasa Tinubu, Atiku da Kwankwaso A Birnin Tarayya Abuja

A sakamakon da hukumar zabe INEC ta sanar a matakin jiha, tsohon gwamnan Legas ya samu kuri'u 298,396, yayin da Atiku Abubakar ya take masa baya da kuri'u 298,396.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Rabiu Musa Kwankwaso, ɗan takarar shugaban kasa a inuwar NNPP mai kayan daɗi ya zo na uku da kuri'u 4,044, yayin da takwaransa na jam'iyyar Labour Party ya samu 1,660, a cewar rahoton Ripples.

Legit.ng Hausa ta tattaro maku yadda sakamakon ya kaya, ga su kamar haka;

Karamar hukumar Anka

APC – 13,467

PDP – 5,358

Karamar hukumar Gummi

APC – 22,745

PDP – 20,702

Karamar hukumar Bukkuyum

APC – 15,812

PDP – 9,914

Karamar hukumar Talata Mafara

APC – 35,384

PDP – 7,472

Karamar hukumar Maradun

APC 21, 274

PDP 5, 829

Karamar hukumar Bakura

APC 34,110

Kara karanta wannan

Ta leko ta koma: Gwamna Ortom ya sha kaye a zaben sanata, dan APC ya lashe zabe

PDP 10,824

Karamar hukumar Shinkafi

APC – 8,692

PDP – 7,517

Karamar hukumar Birnin Magaji

APC – 22,638

PDP – 6,467

Karamar hukumar Kauran Namoda

APC – 25,301

PDP – 17,664

Karamar hukumar Zurmi

APC – 14,651

PDP – 13,081

Karamar hukumar Bungudu

APC – 22,013

PDP – 22,430

Karamar hukumar Tsafe

APC – 24,984

PDP – 17,871

Karamar hukumar Maru

APC – 12,064

PDP – 7,776

Karamar hukumar Gusau

APC – 25,261

PDP – 41,073

A wani labarin kuma Tinubu Ya Kara Shiga Gaban Su Atiku, Ya Samu Nasara a Jihar Neja

Jihar Neja ta shiga cikin jerin jihohin da Bola Tinubu ya samu nasara a zaben shugaban kasan da ya gudana ranar Asabar da ta shige.

INEC a matakin jiha ta bayyana sakamakon da yawan kuri'un da kowace jam'iyyar ta samu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262