'Yan Daba Sun Hana Bayyana Sakamakon Zaɓe a Jihar Plateau
- Ƴan daba a jihar Plateau sun kawo tarnaƙi a wajen tattara sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da na ƴan majalisun tarayya
- Ƴan daban sun tarwatsa jami'an hukumar INEC inda suka hana a bayyana sakamakon zaɓen
- Hukumomin da abin ya shafa sun tabbatar da aukuwar lamarin inda suka yi alƙawarin ɗaukar matakin da ya dace
Jihar Plateau- Ƴan daba sun kai farmaki cibiyar tattara sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da na ƴan majalisu a a mazaɓar Plateau ta Arewa inda suka hargitsa aikin tattara sakamakon zaɓen.
Ƴan daban sun farmaki wajen ne a ranar Litinin sannan suka tarwatsa jami'an hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) da sauran ma'aikatan wucim gadi na hukumar. Rahoton Vanguard
Rigimar ta fara ne lokacin da jami'in tattara zaɓen ɗan majalisar Jos North/Bassa, Nehemiah Sanda, ya bukaci wakilan jam'iyyu da rattaɓa hannu kan sakamakon zaɓen.
Sakamakon zaɓen ya nuna cewa ɗan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Musa Agah, shine ya samu ƙuri'u mafi yawa a zaɓen.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jami'in tattara zaɓen shugaban ƙasa na ƙaramar hukumar Jos ta Arewa, Dr Lazurus Maigoro, ya tabbatar da aukuwar lamarin. Rahoton The Punch
Yayi bayanin cewa lamarin ya kawo tashin hankali sosai a cibiyar tattara sakamakon zaɓen, inda ya ƙara da cewa ƴan dabar sun hana a bayyana sakamakon zaɓen ɗan majalisar tarayya da na sanatan yankin.
“Eh da gaske ne ƴan daba sun farmaki wurin da muke tattara sakamakon zaɓen muna cikin yin aikin mu. Yanzu ya rage INEC ta san abinda zata yi." A cewar sa
Kwamishinan hukumar INEC na jihar, Dr Oliver Agundu, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, yace har yanzu bai samu cikakken bayani ba kan lamarin.
”Bani a wajen da lamarin ya auku, ina can ina ta tattara sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na jiha."
”Amma zan zauna da jami'an da abin da ya shafa, domin samun cikakken rahoto kan lamarin sannan nayi abinda ya dace."
Atiku Abubakar Ya Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa a Jihar Bauchi
A wani labarin na daban kuma, Abubakar ya ba Tinubu tazara mai yawa a zaɓen shugaban ƙasa na jihar Bauchi.
Ɗan takarar na jam'iyyar PDP ya samu nasarar lashe zaɓen shugaban ƙasa a jihar.
Asali: Legit.ng