Tsohon Gwamnan PDP Ya Caccaki Jam’iyya, Ya Jero Abin da Ya Jawo Masu Rashin Nasara

Tsohon Gwamnan PDP Ya Caccaki Jam’iyya, Ya Jero Abin da Ya Jawo Masu Rashin Nasara

  • Ayodele Peter Fayose yana ganin shugabannin jam’iyyar PDP suka jawo rashin nasara a zaben 2023
  • Duk da ba a gama tattara kuri’u ba, Tsohon gwamna a jihar Ekiti ya ce Atiku Abubabakar ya sallama
  • Fayose ya ce babu ta yadda PDP za ta ci zabe bayan ta kori Kwankwaso da Obi, kuma ana rikici da G5

Abuja - Tsohon gwamna a jihar Ekiti, Ayodele Peter Fayose ya yi wasu maganganu a shafin Twitter a ranar Litinin a game da zaben sabon shugaban kasa.

The Cable ta ce Ayodele Peter Fayose ya yi maganganun ne jim kadan bayan an ji Dino Melaye yana babatu a wajen tattara sakamakon zabukan 2023.

Da yake bayani, Ayo Fayose ya jinjinawa Peter Obi da ya yi takara a jam’iyyar LP, ya kuma soki shugabannin PDP da suka gagara kashe wutar rigimar G5.

Kara karanta wannan

Atiku ya Samu Tulin Kuri’u a Delta, Hukumar INEC ta ki Amincewa da su, ta Kawo Hujja

“Na jinjinawa karfin hali da kokarin ‘dan takaran LP a zaben shugaban kasa, Peter Obi, da ya yi abin da ba a taba gani ba a sakamakon zaben nan.
Ba abin mamaki ba ne ganin irin karbuwar da ya yi a wajen ‘Yan Najeriya. Amma kuma dole in caccaki PDP domin ba ta isa ta ce an zalunce ta ba.
Masu jan ragamar jam’iyyar sun san haka za ta faru a dalilin girman kan su da kuma jin sun isa, musamman kuma su ne suka ci amana a zaben 2015.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

- Ayo Fayose

Atiku Abubakar
Atiku Abubakar yana kamfe Hoto: www.thecable.ng
Asali: UGC

Kowa ya yi da kyau, zai ga da kyau

A rayuwar nan duk abin da mutum ya shuka, shi zai girba. Bayan haka, jam’iyyar PDP ta na so ta ci zabe ne a wargaje irin yadda ta ke a halin yanzu?

Kara karanta wannan

Assha: EFCC ta kame daraktan kamfen gwamnan PDP na Arewa da kudade a hanyar zuwa zabe

An kori Kwankwaso, Obi da sauransu daga jam’iyyar, kuma sun ce za su iya ko babu ‘Yan G5.
Ran ka ya dade, Iyorchia Ayu shugaban jam’iyya ya rasa mazabarsa da karamar hukumarsa. Yanzu PDP ta dawo ta na kukan da bai damu ‘Yan Najeriya ba.
Fayose ya ce mafi muhimmanci shi ne wadanda ba su ji dadi ba, su tafi. Lokaci ya yi da za a kyale ‘Yan Najeriya, ya kuma ce yanzu PDP ta rasa farin jininta."

- Ayo Fayose

Tsohon Gwamnan ya ce Obi da aka hana tikiti ya yi wa manyan PDP ritaya, a karshe ya ba Atiku shawara ya karbi sakamakon, ya tafi Dubai ya yi ritayarsa.

‘Dan takaranmu Atiku ya karbi kayi cikin girma, ya lallaba ya tafi Dubai, lokaci ya yi da za a ce sai an jima."

- Ayo Fayose

Atiku ya doke APC a Kaduna

A gefe guda kun ji labari APC ta rasa garuruwan Kaduna ta Arewa, Kaduna ta Kudu, Soba, Giwa, Kauru, Lere, Ikara, Kagarko, Zaria, Sabon-Gari, da Makarfi.

Kara karanta wannan

Karin bayani: 'Yan daba sun sace na'urar aikin zabe a jihar su Buhari da kuma wata jihar

Kananan hukumomin Kudu, Kaura, Kajuru, Jaba, Kachia, Jema’a da Zango-Kataf sun fada hannun Jam’iyyar LP da Peter Obi a zaben shugaban kasa a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng