Tinubu Ya Kara Shiga Gaban Su Atiku, Ya Samu Nasara a Jihar Neja

Tinubu Ya Kara Shiga Gaban Su Atiku, Ya Samu Nasara a Jihar Neja

  • Bayan kammala zaben shugaban kasa ranar Asabar da ta gabata, INEC na ci gaba da bayyana sakamako a matakin jihohi
  • A jihar Neja, Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC mai mulki ne ya samu nasara kan sauran yan takara da kuri'u mafi yawa
  • Baturen zaben jihar ya bayyana sakamakon kuri'un da kowace jam'iyyar siyasa ta samu

Niger - Ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Ahmed Bola Tinubu, ya samu nasara da kuri'u mafiya rinjaye a sakamakon zaben shugaban kasa na jihar Neja.

Daily Trust ta rahoto cewa Tinubu ya lallasa manyan abokan hamayyarsa, Peter Obi, na jam'iyyar LP da Atiku Abubakar na PDP da Rabiu Musa Kwankwaso na jam'iyyar NNPP.

Bola Ahmed Tinubu.
Bola Tinubu ya daga hannu ga masoya Hoto: Bola Tinubu
Asali: Twitter

Tinubu ya lashe kananan hukumomi 21 cikin 25 da ke Neja, yayin da Atiku Abubakar, wazirin Adamawa ya samu nasara a guda 3, Peter Obi ya lashe Suleja.

Kara karanta wannan

Sakamakon Zabe: Peter Obi da Atiku Sun Sha Kashi Hannun Tinubu, An Faɗi Sakamakon Jihar Benuwai

Yayin da yake sanar da adadin kuri'un da kowace jam'iyya ta samu, Baturen zabe na Neja kuma mataimakin shugaban jami'ar Abuja, Farfesa Clement Allawa, ya ce APC ta lashe kuri'u 375,183.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce jam'iyyar PDP wacce ta zo a matsayin na biyu ta samu kuri'u 284,898, Labour Party na da kuri'u 80,452 yayin da New Nigeria Peoples Party watau NNPP ta samu 21,836.

Bayan sanar da wannan sakamako, wakilin jam'iyyar PDP, Honorabul Idris Sani Kutigi, ya yi fatali da sakamakon kuma ya ƙi rattaba hannun rakardar sakamakon.

Ya ce ba bu sakamakon da hukumar da zabe INEC ta sanya a shafinta na yanar gizo-gizo kamar yadda ta yi alƙawari, kamar yadda Channels tv ta rahoto.

Har yanzu dai ana ci gaba da tattara sakamakon zaben shugaban kasa wanda ga gudana ranar Asabar 25 ga wataɓ Fabrairu, 2023.

Kara karanta wannan

Da lam’a: PDP ta ce akwai gyara, bata amince da sakamakon zaben shugaban kasa ba

Tinubu ya yi nasara a jihar Benuwai

A wani labarin kuma Tinubu Ya Baiwa Peter Obi Mamaki, Ya Lashe Zabe da Yawan Kuri'u a Benuwai

An yi hasashen Peter Obi ne zai lashe mafi yawan kuri'un jihar Benuwai saboda goyon bayan da ya samu daga gwamna Samuel Ortom na jam'iyyar PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262