Yanzu Yanzu: Obasanjo Ya Bukaci a Soke Zaben Shugaban Kasa
- Ana tsaka da tattara sakamakon zaben shugaban kasa a matakin kasa, tsohon shugaban kasa ya gabatar da wata bukata a gaban INEC
- Olusegun Obasanjo ya bukaci shugaban hukumar zabe ta kasa, Mahmood Yakubu da ya soke zaben shugaban kasa na 2023
- Obasanjo ya nemi a yi haka don ceto kasar daga annoba da fitinar da ke tunkarota sakamakon zargin magudi a zaben
Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya ce akwai lauje cikin nadi a zaben shugaban kasa na ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu, don haka a soke zaben, jaridar Leadership ta rahoto.
Musamman Obasanjo ya bukaci shugaban zabe ta kasa mai zaman kanta, Farfesa Mahmood Yakubu, da ya ceto Najeriya daga hatsari da annobar da ke shirin faruwa.
Ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa mai taken "Zaben shugaban kasar Najeriya na 2023: Rokon Yin Taka-tsan-tsan da Gyara."
A cewarsa, ba boyayyen lamari bane cewa jami'an INEC a matakin aiki sun yi rashin gaskiya bayan mika rubutaccen sakamako da aka yi magudi da kutse a ciki, Daily Trust ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Obasanjo na goyon bayan Peter Obi na Labour Party
Obasanjo dai ya fito fili ya ayyana goyon bayansa ga dan takarar shugaban kasa na Labour Party, Peter Obi a zaben.
Tsohon shugaban kasar ya ce babu tsarkakke a cikin yan takarar shugaban kasar, amma idan aka kwatanta a bangaren ilimi, da'a da abun da za su iya yi, Obi ya fi su dan dama-dama.
A yayin zaben shugaban kasar na ranar Asabar, Obasanjo ya gaza kawo rumfar zabensa da ke Abeokuta, jihar Ogun ga dan takarar da yake so domin dai Bola Tinubu na APC ya lallasa Obi a akwatin zaben.
An dai rahoto cewa an shiga rudani a cibiyar tattar sakamakon shugaban kasar na kasa a yau yayin da wakilin PDP, Dino Melaye da sauransu suka fita daga wajen, suna masu zargin an yi kutse a tsarin.
Wasikar ta Obasanjo na zuwa ne yan awanni bayan wakilan jam'iyyar sun yi zanga-zanga.
A gefe guda, mun ji cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu shine kan gaba a jihohi 10 da aka sanar da sakamakonsu zuwa yanzu.
Asali: Legit.ng