PDP Ta Lallasa Jam'iyyar APC a Ƙaramar Hukumar Gwamnan Kaduna
- Jam'iyyar PDP ta yiwa APC Bulala a ƙaramar hukumar gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai
- El-Rufai da ɗan takarar gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, sun kasa kawo wa APC ƙaramar hukumar su a zaɓen shugaban ƙasa
- Jam'iyyar PDP ta yiwa APC tazara mai nisa a sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na jihar da aka bayyana
Jihar Kaduna- Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya kasa kawo wa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ƙaramar hukumar sa a zaɓen shugaban ƙasa.
A ƙaramar hukumar Zaria, inda nan ne mahaifar El-Rufai da ɗan takarar gwamnna jihar Kaduna na jam'iyyar APC, Uba Sani, jam'iyyar PDP ta yiwa APC lalas. Rahoton Daily Trust
Jam'iyyar APC na ji a jiki a hannun jam'iyyar PDP a jihar Kaduna, inda ta ke kan gabanta sosai a sakamakon wasu ƙananan hukumomin da aka bayyana.
A ƙaramar hukumar Zaria, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya samu ƙuri'u 62,260. Yayin da Asiwaju Bola Tinubu na APC, ga samu ƙuri'u 41,432.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na jam'iyyar New Nigerian Peoples Party (NNPP) ya zo na uku inda ya samu ƙuri'u 8,729 sannan Peter Obi na Labour Party ya samu ƙuri'u 3,634.
Daga cikin sakamakon ƙananan hukomomi 16 da aka bayyana ya zuwa yanzu, APC tayi nasara ne kawai a ƙananan hukumomi biyu, yayin da PDP ta samu nasara a ƙananan hukomomi tara.
Sannan jam'iyyar Labour Party ta samu nasara a ƙananan hukumomi 16.
Wannan rashin naarar ba zata yiwa gwamnn daɗi ba domin yana daga cikin jigan-jigan gwamnonin jam'iyyar APC, dake marawa Tinubu baya, a takarar da yake yi ta neman ɗarewa kujerar shugabancin ƙasar nan.
Peter Obi Ya Kwashi Garabasar Kuri’un Al’ummar Jihar Enugu a Zaben Shugaban Kasa
A wani labarin na daban kuma, jihar Enugu ta yiwa Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party, ruwan ƙuri'u.
Ɗan takarar ya samu gagarumar nasara a ƙananan hukumomi goma sha bakwai na jihar Enugun, inds ya bar sauran abokan takarar sa a baya.
Asali: Legit.ng