Atiku Ya Lallasa Bola Tinubu, Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa a Yobe
- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya samu nasara lashe zaben jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya
- Atiku ya yi nasara a jihar duk da jam'iyyar APC ce take mulki a jihar karkarshin gwamna Mai Mala Buni
- Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ɗan jihar ne kuma ya samu nasarar lashe kujerarsa ta Sanatan Yobe ta arewa
Yobe - Ɗan takarar shugaban kasa a inuwar jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya lashe zaben shugaban kasa a jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Atiku, haifaffen shiyyar arewa maso gabas, ya lallasa babban abokin adawarsa na jam'iyya mai mulkin jihar Yobe, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na APC.
Jimullan sakamakon zaben wanda ya gudana ranar Asabar 25 ga watan Fabrairu, 2023 ya nuna Atiku ya samu kuri'u 198,567, yayin da Bola Tinubu ya tashi da kuri'u 151,456.
Tsohon gwamnan Kano kuma ɗan takarar shugaban kasa a inuwar New Nigeria Peoples Party watau NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, ne ya zo na uku da kuri'u 18, 270.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jihar Yobe nan ne mahaifar shugaban majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, jigo a jam'iyyar APC, wanda ya samu nasarar lashe kujerarsa ta Sanatan Yobe ta arewa amma ya gaza kawowa Tinubu kuri'un jihar.
Yadda sakamakon zaben shugaban ƙasa daga Yobe ya nuna
APC - 151,459
APGA - 875
NNPP - 18,270
PDP - 198,567
YPP - 630
Tsohon mataimakin shugaban kasan ya samu nasara a jihar Katsina, mahaifar shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari. Haka zalika ya yi nasara a jihar Gombe kuma shi ke kan gaba a jiharsa ta Adamawa kawo yanzu.
Hukumar zabe ta ƙasa mai zaman kanta (INEC) ta bude zauren tattara sakamako daga jihoji jiya Lahadi, amma har ta ɗage zaman zuwa ranar Litinin jiha kaɗai suka kai sakamakonsu.
A wani labarin kuma kun ji cewa Peter Obi na shirin baiwa Bola Tinubu mamaki ya lashe zaben shugaban kasa a jihar Legas
Har zuwa lokacin da aka bayyana sakamakon kananan hukumomi 17, tsohon gwamnan Anambra ne ke kan gaba duk da tazarar ba ta da yawa tsakaninsa da Tinubu.
Sai dai tsohon gwamnan Legas din ya lashe mafi yawan kananan hukumomi amma yana bayan Obi.
Asali: Legit.ng