Sakamakon Zabe: Peter Obi Ya Shiga Gaban Bola Tinubu a Jihar Legas
- Rahoton da ke shigowa ya nuna cewa Peter Obi na shirin lallasa Bola Tinubu a jiharsa ta Legas
- Bayan bayyana sakamakon kananan hukumomi 17, ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar LP ne a kan gaba da yawan kuri'u
- Ana ganin Legas na cikin kusoshin jihohin da Tinubu ke tutiya da su kuma ya yi gwamna tsawon shekaru 8
Lagos - Ɗan takarar shugaban kasa a inuwar Labour Party, Peter Obi, ya shiga gaban babban abokin hamayyarsa na jam'iyyar APC, Bola Tinubu, a sakamakon zaben jihar Legas.
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa kawo yanzu da aka bayyana sakamakon kananan hukumomi 17 cikin na jihar Legas, Peter Obi na kan gaba.
Duk da Tinubu, tsohon gwamnan jihar Legas, ya samu nasara a mafi yawan kananan hukumomi amma yana bayan Mista Obi, wanda ya zarce shi da kuri'u 1,686.
Tinubu ya samu nasara a kananan hukumomi 10, yana da jumullan kuri'u 447,192 kawo yanzu, Mista Obi ya lashe kananan hukumomi 7 amma yana gaba da tazara 'yar kaɗan, yana da kuri'u 448,878.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Tun da farko, bayan bayyana sakamakon kananan hukumomi 12 Bola Tinubu ne a kan gaba amma yayin da ƙarin kananan hukumomi suka ƙara isowa, nan da nan Obi ya sha gabansa.
Sauran manyan masu neman zama shugaban ƙasa, Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP da Rabiu Musa Kwankwaso na jam'iyyar NNPP, har yanzu ba su kai ga lashe ko karamar hukuma ɗaya ba.
Kananan hukumomi 10 na Tinubu ya samu galaba sun haɗa da, Agege, Apapa, Badagry, Epe, Ibeju-Lekki, Ifako-Ijaiye, Ikorodu, Lagos Island, Lagos Mainland, da kuma Surulere.
A ɗaya bangaren kuma, Mista Obi ya samu nasara a kananan hukumomin da suka kunshi, Ajeromi-Ifelodun, Amuwo-Odofin, Eti-Osa, Ikeja, Kosofe, Oshodi-Isolo, da Somolu.
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa ana dakon sakamakon ragowar kananan hukumomin Mushin, Ojo, da Alimosho kafin tantance wanda ya yi nasara a Legas.
APC ta yi nasara a jihar Benuwai
A wani labarin kuma Tinubu Ya Baiwa Peter Obi Mamaki, Ya Lashe Zabe da Yawan Kuri'u a Benuwai
Duk da goyon da Peter Obi da samu daga gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom, bai iya kawo masa mafi yawan kuri'un jihar ba a zaben shugaban kasan da ya gabata.
Asali: Legit.ng