Kanin Tsohon Shugaban Kasa ‘Yar’adua Zai Zama Sanatan Katsina a Majalisar Dattawa
- Kanal Abdulaziz Yar’adua mai ritaya zai zama ‘Dan majalisar dattawa nan da ‘yan watanni
- A zaben Sanatan Katsina ta Arewa, Jam’iyyar APC ta iya rike kujerar ta da kyar a zaben 2023
- Abdulaziz Yar’adua wanda aka fi sani da Audu Soja, ya doke ‘dan takaran PDP, Aminu Sirajo
Katsina - Kanin Marigayi Umaru Yar’adua ne wanda aka tabbatar a matsayin wanda ya lashe zaben ‘dan majalisar dattawa na tsakiyar Katsina.
Kanal Abdulaziz Yar’adua wanda aka fi sani da Audu Soja ya yi galaba a jam’iyyar APC mai mulki. Premium Times ta tabbatar da wannan labari.
Abdulaziz Yar’adua ya lashe kuri’u 153, 512 a jam’iyyar APC yayin da babban abokin karawarsa na PDP, Aminu Sirajo ya tashi da kuri’u 152,140.
Malamin zaben da ya sanar da sakamakon a ranar Lahadi, Aminu Kankia ya bayyana nasarar APC. 'Yan PDP ba su yarda da sakamakon ba.
NNPP da PRP sun zo na 3, 4
Vanguard ta ce Aminu Kankia ya sanar da cewa Gambo Abubakar wanda ya tsaya a jam’iyyar NNPP ya samu kuri’u 16, 005 a zaben majalisar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
‘Dan takaran jam’iyyar adawa ta PRP, Aminu Gide shi ne ya zo na hudu a zaben da kuri’u 781.
Kafin shigarsa siyasa, Abdulaziz 'Yar’adua ya yi aiki a gidan soja, ya yi ritaya da kan shi a matsayin Kanal. 'Yar’adua ya nemi tikiti a 2019, bai dace ba.
Tsohon Sojan zai canji Sanata Kabiru Barkiya wanda ya karbi kujerar 2019.
APC za ta samu Sanatoci 3
Legit.ng Hausa ta samu rahoto cewa Ahmad Babba Kaita ya rasa kujerar ‘dan majalisar dattawa a jam’iyyar PDP, Nasiru Zango ne ya doke Sanatan.
Nasir Sani Zango na APC ya samu kuri’u 174,523 yayin da Sanata Ahmed Babba Kaita ya kare da 163,505. Katsina ta Arewa ne yankin Muhammadu Buhari.
Akwai alamu da ke nuna Hon. Muktar Dandutse na jam’iyyar APC zai yi nasara a kujerar Katsina ta Kudu, idan hakan ta faru, APC ta samu Sanatoci uku.
Siyasar Kano sai Kano
Kamar Hon. Alhassan Ado Doguwa zai koma majalisar tarayya, labari daga Kano ya zo cewa Hon. Abdulkadir Tijjani Jobe ya sake lashe zabensa a NNPP.
A zaben bana, Jam’iyyar tsohon Gwamna, Rabiu Kwankwaso watau NNPP tayi wa APC mai mulki tun 2015 illa duk da ba ta dade da shigowa Kano ba.
Asali: Legit.ng