Zaben 2023: Obasanjo, Adamu, Datti, Lawan Da Manyan Mutanen Da Suka Fadi a Rumfar Zabensu
Yayinda aka gudanar babban zaben Najeriya, akwai wasu manyan yan siyasa da suka gaza kawowa yan takarar da suke goyon bayan rumfunan zabensu.
Rashin kawo wannan akwatuna ba wai yan siysar kawai zai shafa ba, harma da sauran masu neman takarar a jam'iyyunsu.
Ga jerin sunayen manyan yan siyasa da wuraren da suka sha kaye a kasa:
1. Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo
Obasanjo ya gaza kawowa Peter Obi rumfar zabensa da ke jihar Ogun inda jam'iyyar Labour Party ta sha kaye da kuri'u tara, yayinda Asiwaju Bola Tinubu ya lashe kuri'u 56.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
2. Abdullahi Adamu
Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adamu Abdullahi ya gaza kawowa jam'iyyarsa rumfar zabensa da ke jihar Nasarawa inda dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi ya yi nasara.
Yayin da Bola Tinubu ya samu kuri'u 85 a rumfar, Obi ya tashi da kuri'u 132.
3. Gwamna Godwin Obaseki
Gwamna Obaseki na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya gaza kawowa Atiku Abubakar rumfar zabensa da ke karamar hukumar Oredo, gudunma ta 4, akwati mai lamba ta 19 makarantar firamare ta Emokpae Model.
Peter Obi na Labour Party ne ya lashe rumfar zaben da kuri'u 105. PDP ta samu 55 yayin da Tinubu ya zo na uku da kuri'u 27.
4. Datti Baba-Ahmed
Abokin takarar Obi, Datti Baba-Ahmed, ya fadi rumfar zabensa inda Atiku na PDP ya yi nasara a mazabar tasa ta PU 021 Tundun Wada, Zariya da ke jihar Kaduna.
PDP ta samu kuri'u 102 wajen lashe zaben, APC ta samu kuri'u 98 yayin da NNPP ta samu 11.
Akin Osuntokun
Darakta Janar na kwamitin yakin neman zaben Obi, Osuntokun, ya gaza kawowa jam'iyyar LP rumfar zabensa.
A sakamakon zaben, APC ta samu kuri'u 14,516 yayin da LP ta samu 391.
A halin da ake ciki, PDP ta samu kuri'u 4,318 yayin da NNPP ta samu kuri'u 10.
5. Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan
Lawan ya gaza kawowa Tinubu rumfar zabensa mai lamba 001B, makarantar firamare da Katuzu da ke Gashua, jihar Yobe.
Kamar yadda sakamakon ya nuna, Tinubu ya samu 107 yayin da Atiku ya samu 186.
6. Boss Mustapha
Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya gaza kawowa jam'iyyar APC rumfar zabensa.
Atiku Abubakar ya samu kuri'u 90 yayin da Tinubu ya samu kuri'u 40, Labour Party ta tashi da kuri'u 23.
PDP za ta karbi sakamakon zabe da zuciya daya
A wani labarin kuma, gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal ya bayyana cewa jam'iyyarsu ta PDP ta yarda cewa Allah ke ba da mulki ga wanda ya so don haka za su karbi sakamakon da imani.
Asali: Legit.ng