Mutum Biyar Sun Jikkata Yayin da Yan Ta’adda Suka Farmaki Masu Zabe a Borno – Yan Sanda
- Rundunar yan sandan jihar Borno ta magantu a kan farmakin da yan ta'addan Boko Haram suka kaiwa masu zabe a yankin Gwoza a ranar Asabar
- Mutum biyar da suka hada da mata biyu da maza uku ne suka jikkata a harin kamar yadda Kwamishinan yan sanda a jihar ya sanar
- Mista Abdu Umar ya ce dakarun rundunar sojoji da ke yankin sun yi nasarar budewa mayakan kungiyar ta'addancin wuta
Borno - Rundunar yan sanda a jihar Borno ta tabbatar da cewar mutane biyar sun jikkata a wani hari da mayakan Boko Haram suka kai karamar hukumar Gwoza ta jihar.
Kwamishinan yan sanda a jihar, Mista Abdu Umar, ya tabbatar da lamarin a wata hira da kamfanin dillancin labaran Najeriya a ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu a Maidugudri.
Ya ce mayakan kungiyar ta'addancin sun yi ta harbin bindiga daga saman Mandara inda suka saita harinsu kan masu zabe lamarin da ya yi sanadiyar da mutum biyar suka jikkata, jaridar The Nation ta rahoto.
Har ila yau, Umar ya bayyana cewa wadanda abun ya ritsa da su sun hada da mata biyu da maza uku.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Umar ya ce:
"Kokarin sojojin da ke cikin yankin da abun ya faru ya taimaka wajen fatattakar yan ta'addan inda suka tursasa masu tserewa saboda sun ji zafin wuta."
Zaman lafiya ya dawo yankin sannan an kwashi wadanda suka jikkata zuwa asibiti
Kwamishinan yan sandan ya ce tuni zaman lafiya ya dawo yankin inda har aka ci gaba da zaben yayin da aka kwashi wadanda abun ya ritsa da su zuwa asibiti don jinya.
Gobara ta tashi a babbar kasuwar Maiduguri
A wani labari na daban, mun ji cewa al'ummar garin Maiduri, babban birnin jihar Bono dun wayi gari da wata mummunar annoba na konewar shahararriyar kasuwar nan ta 'Monday Market'.
Lamarin wanda ya afku da misalin karfe 2:00 dare wayewar garin Lahadi, 26 ga watan Fabrairu, ya yi sanadiyar konewar daruruwan shaguna tare da janyo asarar dukiya ta miliyoyin nairori.
Jami'an hukumar kwana-kwana na jiha da ta tarayya sun yi hadaka a kokarinsu na shawo kan al'amarin wanda ba a san menene ya haddasa tashinsa ba.
Asali: Legit.ng