2023: Bola Tinubu Ya Lashe Zaben Kananan Hukumomi 10 a Jihar Ekiti
- Baturen zabe na jihar Ekiti, Farfesa Akeem Lasisi, ya fara karban sakamakon zaben shugaban kasa daga kananan hukumomi
- Zuwa yanzu ya tattara sakamako guda 10 kuma ɗan takarar jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ne ya samu nasara
- A jiya Asabar 10 ga watan Fabrairu, 2023, yan Najeriya suka futa suka zabi wanda zai gaji shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari
Ekiti - Hukumar zabe ta ayyana Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ɗan takarar shugaban kasa a inuwar jam'iyyar APC, a matsayin wanda ya lashe zabe a kananan hukumo 10 a jihar Ekiti.
Baturen zaben INEC na jihar kuma shugaban jami'ar lafiya ta tarayya da ke Ila Orogun, jihar Osun, Farfesa Akeem Lasisi, shi ne ya bayyana sakamakon yankunan.
Ya ce Tinubu ya samu nasara da kuri'u mafiya rinjaye a waɗan nan kananan hukumomin yayin da Atiku Abubakar, na jam'iyyar PDP ke yake masa baya a matsayin na biyu.
Rahoton Daily Trust ya nuna cewa tsohon gwamnan Anambra kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar Labour Party, Peter Obi ne ya zo na uku, sai kuma Kwankwaso na NNPP.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Legit.ng ta haɗa maku sakamakon zaben daga kananan hukumomin guda 10, gasu kamar haka;
Karamar hukumar Efon Alaaye
APC 5873
LP 125
NNPP 03
PDP 2521
Ƙaramar hukumar Gboyin
APC 11,969
LP 245
NNPP 11
PDP 4178
Karamar hukumar Ijero
APC 12628
LP 373
NNPP 06
PDP 5731
Karamar hukumar Ikere
APC 11659
LP 910
NNPP 24
PDP 7198
Karamar hukumar Ise-Orun
APC 11415
LP 497
NNPP 10
PDP 2734
Karamar hukumar Ido/Osi
APC 11917
LP 782
NNPP 14
PDP 7476
Karamar hukumar Irepodun/Ifeodun
APC 14265
LP 544
NNPP 24
PDP 5516
Karamar hukumar Ekiti ta yamma
APC 14516
LP 391
NNPP 10
PDP 4318
Karamar hukumar Moba
APC 12,046
LP 246
NNPP 11
PDP 5847
Karamar hukumar Ikole
APC 15465
LP 779
NNPP 11
PDP 10198
A wani labarin kuma Atiku Ya Lallasa Tinubu a Daya Daga Cikin Akwatin Gidan Gwamnatin Kaduna
Duk da gwamna El-Rufai na jihar Kaduna mamba ne a APC amma hakan bai hana mutanen cikin gwamnatin jihar su juya wa Bola Ahmed Tinubu baya ba.
A ɗaya daga cikin akwatun gidan gwamnatin, Atiku Abubakar na PDP ya samu nasara kan Tinubu, Obi da Kwankwaso.
Asali: Legit.ng