Wata Mai Juna Biyu Ta Yanke Jiki, Ta Rasu a Kan Layin Zabe a Zamfara

Wata Mai Juna Biyu Ta Yanke Jiki, Ta Rasu a Kan Layin Zabe a Zamfara

  • Allah ya yi wa wata mata mai juna biyu rasuwa yayin da take jiran layi domin ta jefa kuri'arta a yankin Tsafe, jihar Zamfara
  • Rahotanni sun nuna cewa matar mai suna, Shamsiyya Ibrahim, ta yanke jiki ta faɗi, ana yi saurin kaita Asibiti amma lokaci ya yi
  • Lamarin mara daɗi ya faru ne a ranar Asabar 25 ga watan Fabrairu, 2023 yayin da zaben shugaban ƙasa ya gudana

Zamfara - Wata mata mai ɗauke da juna biyu, Shamsiya Ibrahim, ta yanke jiki ta faɗi yayin da take jiran layi ya zo kanta ta kaɗa kuri'a a yankin Tsafe, jihar Zamfara ranar Asabar.

Channels tv ta tattaro cewa lokacin da ta yanke jiki ta faɗi a kan layin zaɓen, mutane sun yi hanzarin kai ta babban Asibitin Tsafe don ceto rayuwarta amma aka tabbatar rai ya yi halinsa daga isa.

Kara karanta wannan

2023: INEC Ta Ɗage Lokacin Zabe a Jihohin Najeriya 16? Gaskiya Ta Bayyana

Taswirar jihar Zamfara.
Wata Mai Juna Biyu Ta Yanke Jiki, Ta Rasu a Kan Layin Zabe a Zamfara Hoto: channelstv
Asali: UGC

Bayanai sun nuna cewa Shamsiyya ta taso daga garin Kotorkwashi da ke yankin ƙaramar hukumar Bungudu zuwa Tsafe, tafiya mai nisan kilo mita 50, don kawai ya kaɗa kuri'arta.

Har zuwa yanzu hukumomi ba su fitar da sanarwa ba kan wannan lamarin mai ɗaga hankali wanda ya auku a ranar zaɓen shugaban kasa da 'yan majalisun tarayya, Vanguard ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A halin yanzun an kullle jefa kuri'a a mafi yawan rumfunan zabe a Najeriya yayin da wasu suka fara fitar da sakamako. INEC ta ɗage zabe a wasu rumfuna zuwa gobe Lahadi.

A jawabinsa na ranar zaɓe, shugaban hukumar zaɓe ta kasa mai zaman kanta (INEC), Farfesa Mahmud Yakubu, ya ce ba bu wanda hukumar zata tauye wa hakkin zaɓe.

A cewarsa, duk wanda ya bi tanadin kundin dokokin zaɓe, ya je rumfarsa kafin karfe 2:30 na rana, babu wanda zai hana shi damarsa ta kaɗa kuri'a ga wanda ya kwanta masa a rai.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Faɗa Ya Kaure Tsakanin Magoya Bayan NNPP da APC a Jihar Kano

Yayin da Legit.ng Hausa ta tuntubi wani mazaunin Tsafe, Abubakar Rabiu Tsafe, ya tabbatar da faruwar lamarin da cewa da karfe 1-2:00 na rana matar ta faɗi.

Ya ce ba wurin zabensu ɗaya ba amma wani da ke wurin ya gaya masa cewa tana tsaye a layi ta yanke jiki ta faɗi, da aka kaita Asibiti suka ce rai ya yi halinsa.

A kalamansa ya ce:

"Wani Wanda suke rumfar zabe guda yake fadaman cewa tana bisa layin zabe misalin karfe daya zuwa biyu sai aka ga ta fadi, daman tana da juna biyu. Sai aka dauketa zuwa asibiti, ana zuwa asibitin ta rasu."

Game da yanayin yadda aka gudanar da zabe, Rabiu ya shaida wa wakilin mu cewa zaben ya gudana lami lafiya a garin Tsafe.

Atiku ya ci zaben akwatin gidan gwamnatin Kaduna

A wani labarin kuma Atiku Ya Lallasa Tinubu a Daya Daga Cikin Akwatin Gidan Gwamnatin Kaduna

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: "Kowane Ɗan Najeriya Zai Kaɗa Kuri'u Idan Ya Yi Abu 1" INEC Ta Yi Jawabi Ana Tsaka da Zabe

A ci gaba da tattara sakamako daga rumfunan zabe, wani abun mamaki shi ne Atiku ya yi galaba a ɗaya daga cikin rumfunan zaben gidan gwamnatin Kaduna.

Gwamna Malam Nasiru El-Rufai na ɗaya daga cikin yan sahun gaba a wurin tallata Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262