Atiku Ya Lallasa Tinubu a Daya Daga Cikin Akwatin Gidan Gwamnatin Kaduna

Atiku Ya Lallasa Tinubu a Daya Daga Cikin Akwatin Gidan Gwamnatin Kaduna

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya samu nasara a wani akwatin gidan gwamnatin jihar Kaduna
  • Gwamna Malam Nasiru El-Rufai na ɗaya daga cikin masu yakin neman zaben Bola Tinubu na sahun gaba
  • Abun mamakin ɗan takarar shugaban ƙasa a APC na uku ya zo a sakamakon zaben wamda tuni aka rattaba masa hannu

Kaduna - Ɗan takarar shugaban kasa a inuwar People’s Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar, ya lashe ɗaya daga cikin rumfunan zaɓen da ke cikin gidan gwamnatin jihar Kaduna.

Atiku ya samu galaba kan babban abokin hamayyarsa na jam'iyya mai mulki, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, a rumfar zaben gidan gwamnatin mai lamba PU 013.

Malam Nasiru El-Rufai.
Gwamna El-Rufai Hoto: Governor Kaduna
Asali: Facebook

Rahoton Daily Trust ya bayyana cewa shugaban malaman zaben da suka yi a rumfar, Kalu kelechi Micheal, ya rattaɓa hannu a kan takardar sakamkon zaɓe.

Kara karanta wannan

Kwankwaso Ya Tashi da Kuri’a 1 Kacal Yayin da Atiku Ya Kawowa PDP Akwatinsa

Sakamakon ya nuna cewa Atiku ya samu nasara da kuri'u 69, yayin da Peter Obi, ɗan takarar shugaban kasa a inuwar Labour Party, ya zo na biyu da kuri'u 48.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon gwamnan jihar Legas kuma ɗan takarar APC mai mulkin Kaduna ya ta shi da kuri'u 40, sai kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar NNPP, Rabiu Kwankwaso, wanda ya samu kuri'u 11.

Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai na ɗaya daga cikin jagororin yakin neman zaben Bola Tinubu, kamar yadda jaridar Leadeship ta ruwaito.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa tuni aka gama kaɗa kuri'a a kusan baki ɗaya rumfunan zabe a Najeriya kuma sakamako ya fara fito.

Hukumar zaɓe mai zaman kanta tace zata fara tattara sakamakon shugaban kasa idan Allah ya kaimi Gobe Lahadi 26 ga watan Fabrairu, 2023.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Atiku, Tinubu Sun Tashi a Babu Yayinda Peter Obi Ya Samu Nasarar Farko, Ya Lashe Akwatin Zabensa

Boko Haram ta kai hari a jihar Borno

A wani labarin kuma Mutane Sun Yi Takansu Yayin da Mayakan Boko Haram Suka Kai Hari a Jihar Borno

Rahotanni sun bayyana cewa yan ta'addan kungiyar Boko Haram sun shiga garim Goza, karamar hukumar Goza ana tsaka shirye-shiryen fara zaben shugaban ƙasa.

Sarkin Goza ya ce maharan sun raunata mutane biyar, an tafi da su Maiduguri domin kula da lafiyarsu. Duk da haka an ci gaba da zaɓe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262